Saudiyya zata gina matatar mai a Najeriya

0

Karamin Ministan Harkokin Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa Najeriya na na duba yiwuwar neman agajin kasar Saudi Arabiya ta hada hannu a gina mamatar man fetur a kasar nan.

Ya ce gwamnatin tarayya har ma ta dukufa tattaunawa da jami’an kamfanin Saudi Aramco na Saudiyya, domin jawo hankalin sa ya amince ya zuba jari a farfado da matataun mai na Najeriya wadanda suka mutu, domin a dawo da tace fetur da gas a Najeriya.

Kachikwu ya yi bayanin ne a gidan talbijin na Bloomberg ranar Laraba da ta gabata, a kan taron da ya halarta a Riyadh, babban birnin kasar Saudi Arabiya.

Duk da alkawarin da gwamnati ta yi, har yau ta kasa farfado da matatun mai da suka durkushe.

Har yanzu ana shigo da fetur ne daga waje, bayan an loda shi an fitar da shi an tace.

Amma kuma hamshakin attajirin nan Aliko Dangote ya na gina katafaren kamfanin matatar mai a Lagos, wadda ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya.

Wannan ya na sa a kasar ana fatan zai saukaka tace mai yadda ba sai an rika fita da shi zuwa kasashen waje ana tacewa ba.

Share.

game da Author