SATAR JARABAWA: Dubban daliban da suka zauna jarabawar UTME ba za su samu sakamakon su ba – Shugagan JAMB

0

Dubun daliban da zauna jarabawar UTME, ta shiga jami’o’i, wadda aka gudanar kwanan baya, ba za su samu sakamakon suba.

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka, sakamakon abin da ya kira samun su da laifin satar jarabawa.

Haka ya furta a Lagos, yayin da ya ke bayani lokacin da aka damke wasu yara biyu a Lagos, masu kwamfutocin cibiyar bibiyar jarabawa.

Sun bayyana cewa sun saida takardun tambaoyin jarabawa da amsoshin su na boge ga jama’a masu dimbin yawa.

Cibiyar mai suna Risk Global Company Limited, wadda ke da ofishi a lamba 300, Titin Ikorodu, a Anthony Village, mallakar wani tsohon ma’aikacin banki ne mai suna Emeka Ukpai.

Wadanda ake zargin Godswill Ukpai da David Ukpai, wa da kani ne, sun kuma tabbatar da cewa sun dauki hotunan tambayoyin jarabawar JAMB a cibiyar mahaifin na su.

Sun ce sun sayar wa wani mai wata cibiyar koya wa matasa yadda ake amsa tambayoyin JAMB da ke Legas. Sunan cibiyar Embassy.

Mahaifin na su ya ce ya na nadamar abin da yaran na sa suka aikata. Amma kuma ya ce tunda sun girma, sai su je a gurfanar da su a kotu, shi babu abin da ya shafe shi.

A kan wannan badakala an kama mutane da dama.

A wani jikon kuma, JAMB ta bada sanarwar kama kimanin sojojin haya 100, wadanda suka karbi kudaden jama’a suka zauna musu jarabawa daban-daban.

Share.

game da Author