Sarakunan Zamfara sun kalubalanci ministan tsaro Mansur Dan Ali wanda dan asalin jihar ne da ya bayyana sunayen sarakunan da ya ce wai suna hada baki da maharan dake kai hare-hare a jihar Zamfara suna azabtar da mutanen jihar.
Shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara, Maimartaba sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad ne ya bayyana matsayar sarakunan bayan wani ganawar gaggawa da suka yi a garin Gusau.
Sarkin Anka ya bayyana cewa rashin bayyana sunayen wadannan sarakuna zai tabbatar da cewa minista Dan Ali makaryaci ne kuma yayi haka ne domin ya ci mutuncin sarakunan jihar.
Bayan haka sarakunan sun koka kan yadda jiragen saman sojin Najeriya ke kai hare-hare kan mutane ba maboyar mahara ba.
Sarakunan sun ce mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba ne ake jefa wa bama-bamai a kauyukan Zamfara.
Sai dai kuma rundunar sojin saman ta maida wa sarakunan martani inda ta karyata wannan zargi.
Rundunar ta ce sai da ta samu bayanai akan inda ta rika jefa bam.
Tace wannan zargi ba daidai bane.