SANKARAU: Illolin ta, Yadda Za a Kiyaye da Alamun Kamuwa da ita

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa akalla mutane 44 sun rasu a dalilin kamuwa da sankarau a kasar nan.

Hukumar ta kuma bayyana cewa daga cikin mutane 395 din da aka gwada an gano cewa mutane 43 na dauke da cutar.

Rahotanin hukumar sun kuma nuna cewa akalla mutum daya ya kamuwa da cutar a jihohin Anambra, Bauchi, Bayelsa, Borno, Ebonyi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kwara, Niger, Sokoto, Yobe da Zamfara.

Bayan haka Shugaban cibiyar kiwon lafiya na matakin farko dake jihar Neja Usman Ndanusa ya bayyana cewa cutar sankarau ta yi ajalin mutane takwas a karamar hukumar Borgu dake jihar.

Ya bayyana cewa abin da ya fi damun suna jihar shine yadda mutane ke tyafiya ba tare da sanin yadda cutar take ba sannna kuma karancin magani da ake fama da shi.

” A wannan shekarar wannnan cibiya bata yi wa koda mutum daya ne allurar rigakafi ba saboda ba su. Sannan har yanzu akwai mutanen da suka canfi cutar ko kuma suke ganin harbi ne daga iskokai a mai makon neman magani a asibiti da zaran anji ba dadi a jiki. Sannan kuma ya yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin guje wa kamuwa da cutar domin hana yaduwarta.

Hanyoyin kiyaye kamuwa da sankarau

1. A rika cin abincin da za su inganta kiwon lafiyar mutum.

2. Tsaftace jiki na da matukar muhimmanci wajen samun kariya daga cutar.

3. A rika yawan shan ruwa akai-akai ba sai mutum yana matukar jin kishi ba

4. A tabbatar dakunan da ake kwanciya babu matsalolin rashin iska da cinkoson mutane.

5. A rika yawan samun hutu sannan kuma duk klokacin barci a yi shi da kyau.

6. Yin allurar rigakafi.

7. Hanzarta zuwa asibiti da zaran ba a jin dadi a jiki.

8. A guji cin danyen nama da shan dayanen madara musamman ga mata masu ciki.

Alamun kamuwa da Sankarau

1. Yawan yin atishawa musamman ga yara kananan.

2. Kumburin madigar yaro.

3. Rashin iya cin abinci.

4. Sandarewar wuya.

5. A rika Suma.

6. Mutum ya rika Rudewa.

7. Zazzabi

8. Yawaita yin amai.

9. Rashin samun isasshen barci

10. Ciwon kai.

Ilollin dake afkawa wa kiwon lafiyar mai dauke da cutar.

1. Mutum yaka iya zama kurma idan ba gaggauta yin magani ba.

2. Za a rika yawan yin mantuwa.

3. Sankarau na hana kaifin kwakwalwa.

4. Sankarau na yi wa kodar mutum lahani

5. Mai dauke da cutar zai rika yawan suma.

Share.

game da Author