Sanata Kabiru Gaya na Shiyyar Kano ta Kudu ya fito takarar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wadda za a kaddamar cikin watan Yuni.
Gaya, wanda wannan ne zai kasance zangon sa na hudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana aniyar sa ta takarar a jiya Alhamis, inda ya ce shi ne dan majalisar dattawan da ya fi saura dadewa a Shiyyar Arewa maso Yamma.
Gaya wanda ya sake lashe zabe a karkashin APC, shi ne Shugaban Kwamitin Ayyuka a Majalisa.
Ya taba rike mukamin gwamnan Kano a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, sannan kuma ya taba rike shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.
Ya fito takara ne a daidai lokacin da ake ta yada ji-ta-ji-ta cewa APC za ta mika takarar mataimaki ga sanatocin da ke shiyyar Kudu-maso-gabas.
Gaya ya shaida wa manema labarai cewa shiyyar Arewa maso yamma ce ya dace ta samar da Mataimakin Shugaban Majalisa, tunda a shiyyar ce aka fi bai wa jam’iyyar APC ruwan kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin 2019 diin nan.
Ya ce an rigaya an mika mukamin Kakakin Majalisar Tarayya ga Kudu maso yamma, ita kuma shiyyar Arewa maso gabas an ba ta Shugaban Majalisar Dattawa. Sai Arewa ta Tsakiya kuma aka ba ta mataimakin kakakin majalisa.
“To kun ga idan aka yi la’akari da irin rabon mukamai da aka yin a majalisa, shiyyar Arewa maso yamma ta tashi babu komai kenan. Ni kuma ni ne sanatan da ya fi saura dadewa a majalisar wa wannan shiyya. Don haka ya kamata mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya fito daga shiyyar mu kenan.” Inji Kabiru Gaya.
Gaya ya ce ai ba wani abu ba ne, don Arewa maso yamma ta fitar da Shugaban Kasa, sannan kuma ta samu Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.