Sakaci da shan maganin cututtukan dake kama al’aura na haddasa Kanjamau

0

Kwayoyin cututtuka na ‘Bacteria’ dake kama al’auran mace ko namiji ne ke kawo cututtukan da ke kira cutar sanyin dake kama gaba sannan kin shan magani domin kawar wannan cuta ka sa mutum yaji sha’awar mace ko na miji ya ko ta fita a ran sa ko ranta kuma yana kawo rashin haihuwa da kuma haihuwar bakwaini baya ga tsautsayin iya kamuwa da Kanjamu.

Akan kamu da cutar sanyi ne ta hanyar jima’I, rashin tsaftace jiki musamman al’aura da amfani da bandaki mara tsafta.

Ire-iren cutar sanyi sun hada da chlamydia, gonorrhoea, hepatitis B, syphilis, Herpes da sauran su sannan alamun cutar sun hada da kaikayin gaba, ciwon ciki da mara ga mace, warin baki, jiri, gaban mutum zai rika fitar da ruwa mai wari, kankancewar gaban namiji da sauran su.

Bincike ya nuna cewa mutane sama da miliyan daya na kamuwa da wannan cuta a kullum sannan rashin sani da gudun nuna wariya na daga cikin matsalolin dake sa cutar ta yi ta yaduwa.

Likitocin sun bayyana cewa ba kowani irin cutar sanyi ba ne ke nuna alamu idan an kamu da shi. Sun yi kira da arika gaggauta zuwa asibiti domin sanin me ke damun mutum.

Sannan ma’aikatan asibitin sun yi kira ga mutane da su guji shan maganin kawar da wadannan cututtuka ba tare da izinin likita ba ganin cewa shan maganin ba tare da izinin likita ba na da matsala matuka.

Hanyoyin guje wa kamuwa da wadannan cututtuka:

1. Tsaftace jiki musamman al’aura.

2. Gujewa amfani da ban dakin da shi da tsafta.

3. A guji samun abokin jima’I fiye da daya.

4. Yin amfani da kororo roba a lokacin da za a yi jima’i.

5. Yin gwajin cutar.

Share.

game da Author