Hukumar Tsaron Sojoji ta yi Karin hasken abin da ya biyo baya da yammacin jiya Talata, bayan da Boko Haram suka yi yunkurin shiga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Zaratan ‘Operation Lafiya Dole’, Njoka Irabo, ya aiko wa PREMIUM TIMES bayanin cewa, sojoji sun yi gaggawar garzayawa unguwar Maisandare, inda suka ritsa Boko Haram kuma suka rika bin su su na kashewa.
Ya tabbatar cewa an kashe Boko Haram da dama a lokacin da suka yi yunkurin shiga Damaturu, wajen karfe 5:15 na yammacin jiya Talata.
“Maharan sun rude saboda sun ga an fi karfin su. An rika bin su ana kashewa, tare da taimakon sojojin sama da ke a karkashin ‘Operation Lafiya Dole’.
Irabo ya kuma kara da cewa an jiwa Boko Haram da dama rauni, sannan kuma an kwaci bindigogi da wasu makamai daga hannun su.
Cikin malaman da aka samu, akwai: Motocin Tarakta masu daukar manyan bindigogi, sai bingigar harbo jirgin yaki guda biyu, akwai kuwa roket guda daya, sai AK 47 guda 4, samfurin bindigar GPM 1 da kuma harsasai 1,245.
Discussion about this post