Wani abu mafi jin dadi da alfahari da zai shiga kundin nasarar gwamnati gami da jam’iyya mai mulki shine, yunkurin da shugaba Buhari ya yi na rattaba hannu a sabuwar dokar albashi na mafi karancin naira dubu talatin.
Duk da cewar sai da aka kai ruwa rana da taka rawar siyasa ta bayan fage kafin dokar ta kai labari, to amma koma dai wane tudu da gangare aka biyo, a yanzu kowanne ma’aikaci zai iya darawa idan abubuwa ba su sauya salo da fasali ba.

Tarihin dai karin albashi ba wani sabon abu ba ne. Hakanan abubuwa da dama da suke biyowa bayansa, su ma ba sabbi bane. Sai dai abin nazarin shine kallon halin da ake ciki a yanzu, tare da karin albashin daga dubu goma sha takwas zuwa dubu talatin a kudin naira.
Idan za mu fara waiwaye kadan ta fuskoki biyu zuwa uku ta fuskar aiwatarwar, gami da kallon hakan ta fuskar nasararsa a yanayin zamantakewa, ba shakka akwai wata fargaba da rashin tabbas.
Da farko dai sanin kowa ne a cikin jihohi 36 a Najeriya, wadanda suka zartar da dokar mafi karancin albashi na baya ba su wuce daya bisa uku ba. Hakanan wadanda suke samun sukunin biyan albashin duk wata ba tare da wata matsala ba, su ma ba za su wuce kaso biyu bisa biyar na jihohin ba.
Da ace za mu samu sukunin bibiyar dambarwar da kungiyoyin kwadago ke fama da gwamnoni masu yawa a kasarnan akan batun biyan albashi, da ba za mu iya cewa komai a wannan rubutu ba. An kai jallin akwai Jihar da ta ke shafe wata da watanni ba tare da an biya albashi ba. Da yawa daga cikin ma’aikatansu sun shiga wani hali na tsanani, har akwai masu kashe kansu don sun rasa mafutar rayuwa.
Abu na biyu shine, idan muka kalli yawan al’ummar Najeriya, ina kyautata zaton bai fi kaso 10 cikin 100 ne suke aikin gwamnati ba, ko aikin yake shafarsu kai tsaye ta fuskoki da dama.
A yanzu da aka karawa ma’aikatan albashi wacce rawa sauran gama-garin al’umma za su shiga a rayuwa kasancewar kowa da kowa kasuwa daya yake zuwa don siyan kayan abinci da masarufi.
Kar ku manta, a yanzu kowa ya yarda akwai hauhawar farashi, akwai matsin rayuwa, abin da ake siya naira goma a baya, yanzu ya koma naira talatin. Kuma a sunnar Najeriya, karin kudin man fetur da karin albashi su ne kan gaba wajen kara hauhawar farashi na tashin hankali.
Idan kuwa har hakane, sauran mutane da suke fatan samun saukin rayuwa ina za su kama kenan su samu afuwa?
A kasashen da aka ci gaba, akwai tsari na “social security” ko tallafin da ake bawa marasa galihu da marasa aikin yi, don rage zafin rayuwa, to amma mu a Najeriya babu hakan. Amma dai akwai wani tsari da ake bawa wasu tsirarun mutane wasu kudade kamar dubu biyar haka da sunan samun saukin yau. Shin hakan zai taimaka su samu saukin halin hauhawar farashi da za a shiga? Ba tabbas!
Duk da cewar karin albashin ya hada da sauran kamfanoni da masana’antun da suka wuce mutane 25, to amma wannan bukata ita ce ta dace da yanayin da ake ciki a halin yanzu na hauhawar farashi?
Magana ta gaskiya ita ce, a wasu lokutan muna yin wasu abubuwa ne wadanda kai tsaye ba za su amfani ainahin mutanen da ake ikirarin za a yi wa hakan ba. Misali, me ku ke tsammani idan gwamnati ta kudurci aniyar karya farashin duk kayayyakin da talakawan kasa suke amfani da su? Kamar kayan abinci, gine-gine, sutura da su na aikin gona da kiwo ilimi da lafiya da sauransu? Ina ganin sai kowanne talaka ya samu nutsuwa a Najeriya ba ma ma’aikaci kawai ba.
Ana zaune kalau fa, abubuwa suke ta hauhawa da linkuwa ba ji ba gani. Kuma a yau an wayi gari ana ta tsegumin za a fara kokarin cire sauran tallafin man fetur. Ya rayuwa za ta kasancewa bawan Allah da ya ke samun kasa da naira dari biyar a rana guda?
Ya kamata hukuma ta mike ta fahimci gaskiyar halin da ake ciki a kasa. Ku yi bincike sosai, wace kasa ce take batun karin albashi ko tallafin mai a wannan lokaci da muke ciki? Duniya ta yi nisa sosai, a yanzu ana maganar ya za ayi talaka da yake fama da kansa zai samu nutsuwa a cikin lamuransa na rayuwa. Ta hakanne kadai zai ji ya samu kishin kasarsa a cikin ba tare da ya sani ba, kuma ba zai ji sha’awar aikata duk wani laifi da zai sa yaji kunyar hukumomin kasarsa ba.
A karshe, muna kara yin kira ga hukuma m, a daure a dubi hauhawar farashi da samar da sauki, ko tallafi ko rangwame don talaka gama-gari da baya daukar albashi, shi ma ya san gwamnati ta san da zamansa, ba ma’aikata kadai ake kishi ba. Domin idan har aka bar hakan kara-zube, to ba shakka yankin Arewa da yake fama da karancin masu karbar albashin gwamnati ko kamfanoni, zai ci gaba da fuskantar kalubalen da talauci da rashin ilimi ke kyankyasarwa!