Rikici ya barkewa a tsakanin ‘yan kungiyar sa-ka‘Boys Brigade’ matasa a Gombe

0

Rincimi ya barke a cikin garin Gombe, tsakanin matasa da ‘yan Boys Brigade’, bayan sun yi kokarin shiga su kwasu gawarwakin ‘yan kungiyar su da aka kashe a fadan da ya faru lokacin bikin Easter.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa matasan Boys Brigade ne da suka fito daga asibitin kwararrru a cikin jerin gwano, sai matasan gari suka rufe su da jifa, a unguwar Jekadafari.

Wannan farmaki ne ya sa su ma matasan Boys Brigade yunkurin daukar fansa. Har abin ya kai ga kone motocin wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Sai dai kuma jami’an tsaro sun yi saurin kai dauki da gaggawa.

Kakakin Yada Labarai ta ‘yan sandan jihar Mary Malik ta ce babu cikakken rahoton bayanin rikicin tare da ita ko rundunar ta su.

Tun a ranar Easter ne dai wani jami’an FSCDC mai suna Adamu Abubakar ya banke masu jerin gwano da mota, ya kashe mutum takwas.

Shi kuma a nan take aka yin masa taron-dangi, aka kashe shi tare da wani jami’in dan sanda da suke cikin mota daya.

Share.

game da Author