Rashin halartar Tinubu da Fashola kaddamar da ayyukan Gwamna Ambode ya haifar da damuwa

0

Rashin halartar tsoffin gwamnonin Jihar Lagos biyu, Bola Tinubu da kuma Babatunde Fashola wajen kaddamar da ayyukan raya al’umma da Gwamna Ambode ya yi, ya jefa damuwa.

Ranar Laraba da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar bude muhimman ayyukan da Gwamna Akinwunmi Ambode ya gudanar
Cikin ayyukan da Buhari ya bude, har da gyaran babban filin sama na Lagos, motocin bas-bas na sufuti 820, asibiti mai daukar gado 170, wanda asibiti ne na kula da cututtukan al’aurar mata.

Masu sharhin siyasa sun yi wa bude ayyukan kallon cewa wata siyasa ce Ambode ya shirya, domin nuna ayyukan da yay i, a lokacin da ya ke kusa da mika mulki ga Babajide Sanwo-olu, a ranar 29 Ga Mayu, wanda shi ne zababben gwamna a yanzu.

Duk da cewa Shugaba Buhari da sauran jiga-jigan mulkin siyasa sun hallara a wurin, Jagoran APC Bola Tinubu, wanda ya yi gwamnan Jihar Lagos, daga 1999 zuwa 2007, bai halarta ba.

Haka shi ma Ministan Harkokin Gidaje, Ayyuka da Makamashi, Raji Fashola da ya yi gwamnan Lagos daga 2007 zuwa 2015, bai halarta ba.

TSAKANAIN TINUBU, FASHOLA DA AMBODE

Yayin da jam’iyyar APC ta yi kokarin sasanta tsakanin Tinubu, Fashola da kuma Ambode, abin ya ci tura.

An yi ta tunanin akwai zarge-zarge tsakanin su biyun da kuma Ambode, tun bayan da ya hau gwamna bayan wa’adin Fashola.

Sun kuma rika samun rashin jituwa a tsakanin su biyun da kuma gwmnan, abin ya yi ta ruruwa, har zuwa lokacin zaben fidda-gwani na ’yan akarar gwamnan jihar Lagos.

Wasu sun ce yayinn da Tinubu ya ki goyon bayan Ambode, shi ma Fashola bai goyi bayan sa ba, amma kuma bai fito fili ya ce ga wanda zai goyi baya ba.

Sabani ya shiga tsakanin Ambode da Minsita Fashola tun bayan da Ambode ya hau mulki ba da dadewa ba. An ce sabanin na da nasaba a kan wasu ayyuka ga gwamnan ya aiwatar a jihar Lagos.

Tinubu ya goyi bayan Sanwo-Olu, kuma shi ya ci zabe, yanzu shi ke jiran rantsarwa. Manyan APC na jihar da ake kira Tinubu Mandate Group ne suka kware wa Ambode baya.

KADDAMAR DA AIKI CIKIN GAGGAWA

Ziyarar da Buhari ya yi da kuma kaddamar da aikin da ya yi, duk a cikin gaggawa aka gudanar da su. Yayin da wasu ke ganin kokarin gwamnan, wasu kuma na ganin an yi gaggawar kaddamarwar, domin ba a kai ga kammala wasu ba.

Kakakin Yada Labarai na Tinubu, Tunde Rahman, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Tunubu ba ya kasar shi ya sa bai samu damar halarta ba.

Shi kuma Hakeem Bello, Kakakin Yada Labarai na Minista Fashola, ya ce ai ba wani abu ba ne don ministan bai je ba, domin dai Shugaban Kasa shi ne babban bako a wurin, kuma ya halarta.

Share.

game da Author