Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba adalci ba ne ’yan Najeriya su rika auna ci gaban da aka samu a fannin korar rsshawa da sikelin yawan wadanda aka daure.
Ministan Yada Labarai da Inganta Al’adu, Lai Mohammed ne ya furta haka jiya Litinin a wani shiri da aka yi hira da shi a gidan talbijin na TVC News, a Abuja.
Lai ya ce wannan gwamnati ta samu gagarimar nasarar kafa tubalin yaki da cin hanci da rashawa, wanda idan aka juri tafiya, za a samu babbar nasarar da za tac kai ga Najeriya zama kasaitacciyar kasa.
Ministan ya buga misali da nasarar da aka samu a fannin kafa Asusun Bai Daya Tilo na Gwamnati, wato tsarin TSA da kuma shigo da tsarin kwarmato, wanda ake sanar da hukumar wanda ya boye kudade da kuma inda ya boye.
Lai ya kara yin nuni da cewa wannan kandagarkin hana rashawa da gwamnati ta gina ko ta kafa a zangon farko, shi ne zai kara wa gwamnati karfi da kuzarin kokarin yi wa cin hanci da rashawa rubdugu a zango mai zuwa, na biyu.
“A lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, mun iske akwai sama da Asusun Ajiya a Banki na har sama da 2000 a bankuna daban-daban. Wannan ya haifar da rika biyan kudin ruwa masu tarin yawa.
“Sannan kuma gwamnati ba ta da takamaimen sanin adadin kudaden harajin da ke shigo mata.
“Amma ya zuwa yanzu an sama sama da naira tiriliyan 9.3 a asusun gwmnatin tarayya na TSA, wanda da kudaden ne gwamnati ke gudanar da ayyukan raya kasa.’ Inji Minista Lai.