RABON MUKAMAI: Matan APC sun ce ba za a ci yaki da su ba, sannan a bar su da kuturun bawa

0

Kungiyar Mata ’Yan Takara na Jam’iyyar APC sun yi kira da a raba manyan mukaman siyasa na gwamnati da Shugaba Muhammadu Buhari zai fara nada Ministocin sa bayan 29 Ga Mayu.

Shugaban kungiyar, Adedoyin Eshanumi, ta shaida wa manema labarai a jiya Laraba a Abuja cewa, wannan bukata ta su ta zama dole, ganin cewa maza ne suka karbe manyan mukamai har kashi 90 bisa 100 a cikin APC.

Eshanumi wadda ta yi takarar sanata a Jihar Kogi amma ba ta yi nasara ba, ta kara da cewa hanya daya da Buhari zai saka wa mata ita ce a nada da yawan su bisa manyan mukamai.

Ta ce kowa ya san irin rawar da mata suka taka wajen tabbatar da sake nasarar Buhari a zaben 2019.

Shugabar shirya taron mai suna Ann gom-Eze, ta ce an shirya taron ne domin tattauna abubuwan da suka gudana a lokacin zaben 2019, tare da nufin mata za su taru su fito da bukatar su ga wannan gwamnati.

Ta ce idan aka saka musu, to hakan zai kara musu kwarin guiwar sake azama da kuma nunka kokarin da suka yi idan 2023 ta zo.

Share.

game da Author