PDP ta soki Buhari kan tafiyar sa Landan ba tare da damka mulki a hannun Osinbajo ba

0

Jam’iyyar PDP ta soki lamirin tafiyar da Shugaba Mujammadu Buhari ya yi zuwa Landan, ba tare da damka ikon tafiyar da mulki ga Mataimakin sa, Yemi Osinbajo ba.

Har yau dai ba a ce ga dalilin tafiyar ta sa ba, wadda Fadar Shugaban Kasa ta ce sai ranar 5 Ga Mayu ake sa ran dawowar sa.

Sai dai kuma masu lura da al’amurra na ganin cewa Buhari ya je ganin likitocin sa ne a Landan, inda dama ya shafe kusan tsawon shekara daya a can daga cikin shekaru hudu na wannan zango da ya ke a kai.

Ba kamar sauran tafiye-tafiye da ya ke yi ba, a wannan karon bai damka ragamar iko a hannun Mataimakin Shugaban Kasa ba, Yemi Osinbajo, kamar yadda Doka ta Sashe 145 ya dindaya.

Kakakin PDP Kola Ologbondiyan, ya fitar da sanarwar cewa:

“FIcewar Shugaba Buhari daga kasar nan domin fita ziyara ta kan sa, kuma ba tare da damka ikon mulki ba, na nuni da irin yadda APC da gwamnatin Buhari ke watsi da bin dokokin tsarin mulkin kasar nan.”

PDP ta ci gaba da cewa irin wannan tafiya ba tare da sanarwar abin da zai fita yi ba, kuma a lokacin kasa ke fama da matsanancn matsalar tsaro, na abu ne mai fa’ida ba.

Buhari ya fita a lokacin da Boko Haram, masu garkuwa da mutane da kuma fadan kabilanci ke kara kamari a sassan kasar nan.

Na baya-bayan nan shi ne farmakin da masu garkuwa su ka kai jiya Litinin da rana a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A harin sun arce da mutane da dama, ciki har da Shugaban Hukumar Gudanarwar UNEC, Mohammed Mahmood, wanda aka yi garkuwa tare da shi da ‘yar sa bayan kashe direban sa.

PDP ta ce ficewar Buhari ba tare da damka mulki a hannun Osinbajo ba, zai samar da wawakeken gibin da manyan fadawan-ba-ni-na-iya (cabals) za su rika bi su na cikewa.

Share.

game da Author