Ministan Harkokun Noma da Inganta Rayuwar Karkara, Audu Ogbe, ya shawarci matasa da su karfafa zuciyoyin su wajen rungumar noma gadan-gadan, kafin su fara gaganiyar shiga siyasa.
Ogbe ya bayar da wannan shawara ce jiya Alhamis a Abuja, a lokacin da ya halarci rattaba hannu a kan yarjejeniya tsakanin kamfanin NAMEL da kuma MANTRAC Nigeria Limited.
An dai kulla yarjejeniyar ce tsakanin kamfanonin biyu domin samar wa matasa filin noma har hekta 500,000 da za a yi amfani da ita,wajen bunkasa samar da abinci a Najeriya.
Ogbe ya fada ta bakin daraktan ofishin sa, Victor Mayomi cewa ya kamata matasa su yi karatun ta-natsu, su fahimci cewa nauyin wadatar da kasar nan da abinci ya fa rataya ne a wuyan su, ba a wuyan kananan yara ko tsofaffi ba.
“Don haka ni ina jan hankalin ku da ku maida hankali a kan wannan gagarimin shirin noma domin sai da gudummar ku matasa sannan za a iya wadata kasar nan da abinci a nan gaba.”
“Matasa su daina gagariniyar saurin shiga siyasa tukunna. Kamata ya yi su fi bada himma wajen shiga harkokin noma gadan-gadan. Idan suka wadata kasar nan da abinci, sai mu kara jin karfin damka musu amanar kasar nan.” Inji Minista Ogbe.