Sanata Ali Ndume na APC, mai wakiltar Mazabar Barno ta Kudu, ya yi watsi da umarnin da shugabannin jam’iyyar APC suka bayar, cewa Sanata Ahmed Lawan ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa.
A jiya Talata Ndume ya fitar da daftarin ajandodin sa guda 9, wadanda ya ce idan aka zabe shi shugabancin Majalisar Dattawa, a kan su ne zai tafiyar da jagoranci.
Ndume ya ce bai amince a hana shi takara ba, domin shugaban APC ne ya tsaida Lawan, ba tare da tuntubar kowa ba.
Sanata Ndume ya ce ajandar sa ta farko ita ce yin aiki kafada ga kafada da gwamnati, ba tare da yi wa juna katsalandan ba.
Sai kuma ya sha alwashin rage kwarjinin shugabancin majalisa, ta yadda za a rage rububin neman shugabancin.
Ndume cewa ya yi zai zaftare yawancin alfarmar da ke tattare da wanda ke rike da shugabancin majalisar dattawa.
Wata ajanda kuma ita ce zai tabbatar da shimfida ka’idar adadin kwanakin da za a rika tabbatar da cewa a cikin su ne za a tattauna kasafin kudi da kuma kudirori a kammala.
Cewa zai tabbatar da kafa dokar duk abin da za a tattauna ba za a shige sama da kwanaki 90 ba.
Ya ci gaba da cewa zai ja dukkan ‘Yan Majalisar Dattawa a jika, a tafi cikin girma da arziki.
Zai kuma tabbatar da sake gyara dokokin kudade ta yadda za a toshe hanyoyin da kudaden shiga ke sulalewa.
Ndume ya ce za a yi majalisar mai aiki a fili, ba tare da kumbiya-kumbiya ba.