NBC: Lai Mohammed ya amince cewa ya yi gaggawar saka hannu a biyan harkallar kudaden kwangila na naira biliyan 2.5

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya amince cewa bai yi kwakkwaran bincike ba kafin ya yi gaggawar sa hannu a biyan harkallar kudaden kwangila na naira biliyan 2.5 da ta dabaibaye Hukumar NBC a hanlin yanzu.

An sa hannun kwangilar ne inda aka amince a bai wa kamfanin Pinnacle Communications Limited tsabar kudi har naira bilyan 2.5 domin aikin inganta tashar talbijin daga tsohon ya yi (analogue), zuwa na zamani, wato digital.

Lai Mohammed ya shaida wa ICPC cewa ya sa hannun biyan kudin a bisa rahoton da Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin (NBC), Modibbo Kawu ya kai masa, a cikin Mayu, 2017.

Haka dai wadanda ke da masaniya a kan binciken da ICPC ke yi suka tabbatar.

Tun cikin watan Yuni, 2018 ICPC ta fara binciken harkallar. Tuni dai ta gurfanar da Kawu a kotu, a bisa zargin ya yaudari Lai Mohammed wajen shirya harkallar kwangilar.

Kawu dai ya musanta zargin da ake yi masa, tare da cewa a yau Laraba zai halarci kotun tare da Shugaban kamfanin Pinnacle Communications Limited, Lucky Omoluwa.

Pinnacle dai shi ne aka ba naira bilyan 2.5 din da ake ta sa-toka-sa-katsi a kan ta, tun cikin 2017.

Jami’an fallasa harkalla da rub-da-ciki kan kudade sun titsiye Lai Mohammed cikin shekarar da ta gabata su na sheka masa ruwan tambayoyi.

Sai dai kuma bai bari an yi rekodin na muryar sa ya kasa bayar da wani karin bayani fiye da wanda ya bayar cewa ya sa hannu ne kan kwangilar a bisa rahoton amincewa da kamfanin Pinnacle da Modibbo Kawu ya kai masa.

Bai amince an dauki muryar sa ba, sai ya cewa jami’an binciken ya na bukatar karin bayani ko amincewa daga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Haka dai wasu takardun bayani suka nuna, wadanda a yanzu haka PREMIUM TIMES ta ci karo da su.

Wani jami’in EFCC ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Minista Lai Mohammed ya bude musu idanu ya rika yi musu bobbotai, a matsayin sa na babba a cikin gwamnati, kuma Ministan Yada Labarai.

Duk da cewa Lai bai yi wa ICPC hadin kai ba, duk da haka ba ta hada da shi cikin wadanda ta maka kotu ba.

Jami’ar yada labarai ta ICPC, mai suna Rasheedat Okoduwa ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ICPC ba ta hada har da Lai ta maka kotu ba, saboda ya ce yaudarar sa Modibbo Kawu ya yi har ya amince ya sa hannu a kan kudaden da aka bai wa kamfanin Pinnacle.

Amma kuma Rasheedat ta ce idan aka kara samun wasu bayanai a shari’ar da ake wa Kawu, wadanda suka nuna akwai hannun Lai a cikin harkallar, to za a hada da shi a maka kotu.

Wasu takardu da suka fado hannun PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa ba sa hannu kadai Lai ya yi ba, ya sa hannu a kan takardu masu yawa, kuma da shi aka rika tattauna batun kwangilar da kamfanin Pinnacle Communications.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa Lai ya yi wata tafiya zuwa kasashen waje domin yin duba-garin kayayyakin na’urorin sauya tashar talbijin daga tsohon yayi zuwa na zamani.

Kawu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa shi dai bai yi laifin komai ba, kuma bai dauki nauyin laifin sa hannun da Minista Lai Mohammed ya yi ba.

An dai cire naira bilyan 2.5 ne daga naira bilyan 10 da EFCC ta kwace daga Asusun NBC cikin 2016.

Jami’an bincike sun ce an kimshe kudaden a banki, a wata boyayyar hanyar da ta karya tsarin Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya, wato TSA.

Daga baya ne EFCC ta sakar wa NBC da Lai Mohammed kudaden, domin aikin sabunta hanyar kama tashar talbijin ta zamani.

An samu babbar matsala inda takardar da Fadar Shugaban Kasa ta rubuta cikin 2017, ta nuna cewa za a cire kudaden adadin naira bilyan 2.5 daga kudaden NBC da ke cikin Asusun Bai Daya wato, TSA.

Kawu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai bi-ta-da-kullin da ake masa a cikin harkar domin a kawar da shi daga kan kujerar sa.

Wani shahararren lauya mai suna Ogunsanya, ya ce babu yadda za a yi a ce Lai Mohammed ba shi da hannu a cikin wannan harkalla.

A yau ne dai Kawu zai fara gurfana a gaban kotu, a karo na farko.

Share.

game da Author