Nan da watanni 6 Najeriya za tayi sallama da cutar Shan-Inna – Faisal Shuaibu

0

Hukumar kula da da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta kasa ta bayyana cewa tana sa ran nan da watanni shida za Najeriya za at yi sallama da cutar Shan-Inna kwata-kwata.

Shugaban hukumar NPSDC Faisal Shuaibu ne ya bayyana haka a taron manema labarai da yayi domin makon yin rigakafi ta nahiyar Afrika a Abuja.

Faisal ya kara da cewa shekaru uku kenan cutar bata bulloba a ko-ina a fadin kasar nan.

” Mun maida hankali ne matuka wajen ganin ana yi wa yara rigakafin Shan-Inna a ko-ina a fadin kasar nan. Wannan shine babban dalilin da ya sa muka samu irin wannan gagarimar nasara wajen yaki da cutar a kasa Najeriya.

Bayan haka yayi kira ga iyaye da su ci gaba da ba hukumar goyon baya kamar yadda suke yi don ganin inda rigakafin bai kai ba ya kai sannan kuma da taimakawa wajen wayar da wadanda haryanzu basu gamsu da wannan rigakafi ba diomin su rika bari a an yi wa ‘ya’yan su akai-akai.

Share.

game da Author