Najeriya za ta biya naira biliyan 1 ga kamfanonin da aka kwace wa ‘Kodin’

0

Shugaban Hukumar Kula da Nagartar Abinci da Magunguna ta Kasa (NEFDAC), Moji Adeyeye, ta ce gwamnatin tarayya za ta biya diyya ta sama da naira bilyan daya da kamfanonin da aka kwace wa ‘codeine’ sama da shekara daya da ta gabata.

Moji ta yi wannan bayani ne jiya Litinin a Lagos, yayin da ta ke karyata labarin da waya kafar yada labarai ta buga cewa NAFDAC ta ce kashi 70 bisa 100 na magungunan da suka karade kasar nan duk jabu ne.

Adeyeye ta ce an kwace akalla kwalaben ‘Kodin’ miliyan 2.5 a fadin kasar nan. Ta kara da cewa gwamnati na aikin tantance kamfanonin tare da kokarin biyan su diyya.

“Shekara daya kenan tun bayan wani bidiyon da aka yi kan binciken yadda ake shan ‘Kodin’ a matsayin kwayar da ke bugarwa. Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta haramta maganin gaba daya.

Ta ce tun daga lokacin jami’an gwamnati wadanda ke da ruwa da tsaki a fannin da kuma kamfanonin ke ta gudanar da taruka domin kamo linzaminn yadda za a samu mafitar biyan kamfanonin diyya.

“A karshe mun cimma cewa mun dakile kwalabe kimanin miliyan 2.5 daga kamfanoni daban-daban, wadanda kuma hakan ba zai yi wa masana’antun dadi ba, domin ba su ne suka aikata laifin komai.

“A fannin dakile magungunan jabu da kaya ko magungunan da basu da inganci kuwa, mu na kai farmakin samame sau da yawa. Kuma ma’aikatan mu ba su barci, su na sa-ido. Da yawan su kuma su na kwace wadannan magunguna da kaya ta hanyar taimako ko hadin kai da jami’an kwastam.”

Share.

game da Author