NAFDAC ta karyata sanarwan dake cewa wai jabun magunguna sun karade Najeriya

0

A makon da ya gabata ne shugaban hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) Moji Adeyeye ta karyata cewa da akayi wai hukumar ta bayyana cewa mafi yawan magungunan da ake siyarwa a Najeriya duk jabu.

Idan ba a manta ba a ranan 19 ga watan Afrilu jaridar ‘Vangard’ ta wallafa labarin cewa NAFDAC ta ce kashi 70 bisa 100 na magunguna a Najeriya jabu ne.

Gidan jaridar ta wallafa wannan labara mai taken “70% of drugs in Nigerian markets fake — NAFDAC, NDLEA, NOA.’’ A yanar gizo.

A dalilin haka Adeyeye ta yi kira ga mutane,ma’aikatan kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki su yi watsi da wannan rahoto domin babu gaskiya a cikinta.

Ta kuma ce tun da ta dare kujerar shugabancin hukumar ta maida hankali wajen ganin an kau da jabun magunguna a kasar nan.

“A 2005 NAFDAC tare da hadin gwiwar WHO, DFID da kamfanin Pharmacopeia dake kasar Amurka muka gudanar da bincike kan jabun magungunan dake kasar nan inda muka gano kashi 16 bisa 100 ne kawai jabu.

“Tsakanin watannin Janairu 2010 zuwa Afrilu 2012 NAFDAC ta gudanar da bincike domin gano ingancin da maganin kara karfin garkuwa a jiki,zazzabin cizon sauro da cutar siga suke da shi a jihohi 29 da Abuja.

“Sakamakon binciken ya nuna cewa magunguna 371 daga cikin 5790 ne kawai jabu.

“A jihar Legas a watan Mayu 2012 NAFDAC ta gudanar da irin wannan bincike a kan wadannan magunguna da suka kai 235 inda guda tara ne kawai jabu.

“A watan Agusta 2015 daga cikin magungunan zazzabin cizon sauro kashi 96.4 NAFDAC ta gano cewa kashi 23.6 daga cikinsu jabu ne.

Daga nan kuma a 2017 zuwa 2018 bincike ya nuna cewa NAFDAC ta gano cewa kashi 98 bisa 100 na duk magungunan dake Najeriya ingantattu ne.

A dalilin haka hukumar ta karyata rahoton jaridar sannan ta nisanta kanta daga wannan rahoto.

Share.

game da Author