Mutumin da fasto yayi karyan tada shi bayan ya mutu, ya mutu da gaske

0

Brighton Elliot Mayo matashin da limamin wani coci a kasar Afrika ta kudu Alph Lukau ya yi karyan tadawa daga gawa ya rasu da gaske.

Gidajen jaridu dake kasar Zimbabwe sun ruwaito cewa Moyo ya rasu bayan rashin lafiya da ya yi fama da shi tun bayan karyar mutuwa da yai sannan wai aka tada shi daga gawa.

Wani dan uwan Moyo ya bayyana wa gidan jaridar H-Metro cewa Mayo ya rasu a wani kauye mai sun St Luke’s a Afrika ta Kudu sannan sun birne shi ranar Asabar bayan ya yi fama da kunburin ciki na tsawon kwanaki uku.

Bayan an yi kwanaki da tada Moyo daga gawa na karya da Lukau ya yi sai cikin Moyo ya fara kumbura har na tsawon kwanaki uku.

Moyo ya rasu ya bar matarsa daya da dan uwansa.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne limamin cocin dake Johannesburg a kasar Afrika ta kudu Alph Lukau ya yi karyar cewa shi yana da baiwar iya tada gawa.

Wannan labarin dai ya kareda gidajen jaridu da dama da kafafen sada zumunta na yanar gizo a ciki da wajen kasar.

Bayan aikata haka sai limamin cocin Lukau ya fito ya roki gafaran mutane cewa ya yaikata haka ne domin samun mabiya dayawa a cocinsa.

Lukau ya nemi gafaran mutane bayan darektocin kungiyar masu wanke gawa dake kasar ta yi masa barazanar kai sa kara a kotu.

Share.

game da Author