Musabbabin rasuwar matafiya 19 a hatsarin mota a Katsina

0

Hukumar Kula da kuma Kare Hadurra ta Kasa reshen Jihar Katsina, ta tabbar da rasuwar matafiya 19 sannan kuma wasu 38 suka ji raunuka a kan hanyar Daudawa zuwa Sheme, a Karamar Hukumar Faskari.

Kwamandan FRSC na Jihar Katsina, Godwin Ngeuku, ya tabbatar wa manema labarai haka a Katsina.

Ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata da safe, a Daudawa, kilomita kalilan kafin Funtua.

Motar da matafiyan ke ciki samfurin Mitsubishi ce.

Kwamandan ya ce sitiyarin mota ne ya subuce wa direban, har ya kauce hanya, motar ta rika hantsilawa, har ta kashe fasinjojin da dama a nan take.

Ya ce motar mai lamba DKA 654 ZP, ta yi hadarin ne a lokacin da ta ke kan hanyar zuwa Sokoto, dauke da fasinjoji 57.

Ya ce an garzaya da wadanda suka ji raunuka da kuma gawarwakin mamatan a Babban Asibitin Funtua.

Yayin da ya ke ta’aziyya ga iyalan mamatan, Kwamandan na FRSC ya hori direbobi da su rage gudu, su rika tuki da kula, kuma su rage loda wa mota fasinjoji fiye da ka’ida.

MUSABBABIN TAFIYA RISKAR AJALI A HANYA

Wata kwakkwaran majiya da ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa da ita aka yi hidimar kulawa da mamata da kuma wadanda suka ji ciwo a Babban Asibitin Funtuwa, ta ce wadanda suka yi hadarin sun fito ne daga yankin Shiroro, cikin Jihar Neja.

Majiyar dai ya ce bay a son a ambaci sunan sa. Ya kuma tabbatar da cewa bai baro wajen kula da wadanda suka jiraunukan ba, sai bayan Magaribar jiya Juma’a.

“Sun bar gida ne da nufin zuwa garin ’Yankuzo kusa da Tsafe, a Jihar Zamfara. Sun ji labarin wai akwai wani mutum mai bada maganin bindiga a ’Yankuzo. Shi ne suka yi nufin zuwa domin su samo maganin bindigar da aka ce mutumin ya na bayarwa.

“Labarin da mu ka samu shi ne, mahara sun matsa wa yankin da matafiyan su ke a Shiroro. Shi ne mutanen suka gat unda abin hahe-haren sun fara tsamari, gara su samo maganin bindigar da aka ce ana samu a Zamfara.

Share.

game da Author