A dalilin rashin abinci da mazauna sansanin ‘yan gudun hijira dake jihar Bauchi ke fama da shi, yanzu yara da manya dake wannan sansani sun koma suna cin ganyen albasa ne domin su rayu.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai ya ziyarci wannan sansani.
Wani mazaunin wannan sansani Ajidda Ahmed ya bayyana cewa wannan yunwa da suke fama da shi ba yaro ba ba babba ba.
” Babu wani dake kawo mana dauki a wannan sansani. Kowa ta kansa ya ke yi. Ya kaiga ganyen albasa dukkan mu muke ci domin mu rayu. Sannan dama can muna yin bahaya a daji ne gashi an shigo yanayi na damuna. Ruwan sha ma sai ya gagare mu. Abin ya zamo tashin hankali matuka yanzu.
Haka ita ma Aisha Musa ta bayyana wa wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Bauchi. Ta ce wahalar rashin abinci ya tsananta matuka a sansanin inda kowa ke dandana kudar sa.
Shugaban wannan sansani, Bulama Gojja, ya ce mazauna wanna sansani duk ‘yan kabilar shuwa-Arab ne da hare-haren Boko Haram ya fatattaka a kananan hukumomin Marte, Marfa da Marte, Marfa.
Gojja ya roki masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati da ta kawo musu dauki domin su kubuta daga wannan matsala da suka fama da su.