Matsalar tsaro na da nasaba da matsalar fannin ilmi -Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa samar da ingantaccen ilmi na daya daga cikin muhimman matakan zamar da Zaman lumana da kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro a cikin al’umma.

Dangane da haka ne Saraki ya ce matsalar tsaro a kasar nan da ma kowace al’umma na da nasaba da kalubalen da fannin ilmin kasar ke fuskanta.

Bukola Saraki ya yi wannan Karin haske ne a wurin taron Kungiyar Shugabannin Majalisar Dattawa ta Duniya, a Doha, babban birnin kasar Qatar. Taron dai shi ne na 140.

Kakakin Yada Labarai na Saraki, wato Sanni Onogu, ya kara da cewa Saraki ya ce muddin aka bai wa matasa ingantaccen ilmi, to za a dakile yawaitar matasa masu tsatstsauran ra’ayi n da ke kai su ga shiga kungiyoyin ta’addanci.

Ya ce idan aka ginganta ilmi, to al’umma ta gari za ta wanzu tare da rayuwar zaman lumana da cigan kasa.

“Shirin Afuwar Shugaban Kasa ga tsagerun Neja Delta ya yi tasiri sosai. Don ya samar wa matasa guraben karatu, tare da daukar nauyin su jar zuwa jami’o’i.”

Haka kuma shirin cin gajiyar afuwar ya haifar da zaman lafiya a yankin, saboda matasa sun yi watsi da tsageranci, sun kama karatu gadan-gadan.

Ya ce Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yi rawar gani a fannin ilmi, inda ta yi gyara ga dokar UBEC, wato wajibcin samar da ilmi kyauta ga yara har zuwa sakandare.

Sannan kuma ya ce an gyara dokar ta UBEC, yadda jihohi za su ji sauki karbar tallafin kudaden Hukumar Samar Da Ilmin Bai-daya, wato UBEC

A baya sai jiha ta tanadi kashi 50 bisa 100 na kudaden da UBEC za ta ba ta. Amma a yanzu Bukola ya ce an yi wa dokar gyara, kashi 10 bisa 100 kawai jiha za ta gabatar.

Share.

game da Author