Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa sabon tsari dakile matsalar tsaro, ta hanyar kafa ’yan doka a cikin unguwanni da kauyuka da yankuna.
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ne ya bayyana haka a yau Talata a wurin Taron Kungiyar Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya.
An shirya taron ne tare da gudanar da shi a Kaduna, domin tattauna mawuyacin lamarin tabarbarewar tsaro a Arewa.
Dama kuma PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bijiro da sabon tsarin kula da tsaron al’umma a harkoki da mu’amalolin da suka shafe su a cikin yankunan su.
Osinbajo ya ce kafa jami’an tsaron zai bude kofar samar da tsarin sa ido wajen kula da abin da ka je ya zo dangane da sha’anin tsaron jama’a.
Ya ce kafa wadannan sabbin jami’an tsaro ba zai dauke iko da karfin jami’an ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ba.
A na sa bangaren, Sufeto Janar Adamu cewa ya yi wadannan jami’an tsaro da za a kafa a cikin jama’a, za su taimaka wajen ganin an samu gagarimar nasarar tsare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma kawar da barazanar tashe-tashen hankula a cikin al’umma.
Adamu ya kara da cewa wannan sabon tsarin kawar da barazanar tsaro, zai kai ga kafa jami’an da aka fi sani da ‘yandoka, wato ‘Special Constables’.
Ya ce an dauko wannan samfur din tsarin magance kalubalen tsaro ne daga tsarin ‘yan sandan Ingila.
Sannan kuma ya ce za a tsara su ta yadda za su tafi tare da tsarin jami’an tsaro na gargajiya a Arewacin Najeriya.
“Wannan tsari na ‘yandoka za a dauko su ne daga cikin al’umma, kuma zai kasance aiki ne na sa kai a matsayin su na ’yan sandan cikin unguwa, jama’a ko karkara. Amma kuma za su kasance su na karkashin ’yan sanda ne.
Discussion about this post