Matsananciyar matsalar rashin ruwan sha ta addabi mazauna Lokoja, babban birnin Jihar Benuwai.
Hakan kuwa ya biyo bayan sanadiyyar kulle babbar cibiyar da ake tace ruwar garin da aka yi tun a ranar 27 Ga Maris.
Wakilinmu da ya kai ziyara wasu sassan birnin jiya Litinin, ya ruwaito yadda matsalar ta shafi unguwannin gidajen jama’a da kuma yankunan da ake gudanar da kasuwanci.
Wakilin mu ya ruwaito cewa cibiyar tace ruwan wadda aka gina a kan kudi naira bilyan 12, ta na tace litar ruwa har milyan 600 a kowace rana, domin bukatar mazauna Lokoja da kewaye.
Sannan kuma matsalar ruwan ta shafi masu tacewa da saida ruwan cikin leda, wanda aka fi sani da ‘pure water’.
Karancin shi kan sa ‘pure water’ din ya tsananta ne saboda masu sayar da shi ko tace shi, su ma sun dogara ne daga ruwan da ake rabawa daga babbar cibiyar tara ruwa da tace shi ta Lokoja.
Da yawan masu tace ruwan sun daina saboda karancin ruwan. Su kuma saura da ke samun ruwa hajaran-majaran, sun kara kudin ruwan daga naira 100 zuwa naira 100 kowace leda.
Wakilin mu ya lura da cewa a yanzu ‘yan garuwa ne ke cin kasuwar su a birnin Lokoja, saboda akasarin jama’a sun dogara ne da sayen ruwa a hannu ‘yan garuwa din, saboda karancin ruwan famfo.
A halin yanzu, kurar ruwa daya mai cin jarka lita 25 guda 12, wadda a da ake sayarwa naira 300, a yanzu ta kai 350.
Sai dai su kuma mazauna yankunan Kabawa, Madabo, Anguwar Kura, Contonment, Tsohuwar Kasuwa da sauran yankuna da dama, sun koma sun a gangarawa Kogin Neja sun a kamfato ruwa domin amfanin yau da kullum.
Da ya ke magana a kan matsalar ruwan Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Ruwan Jihar Kogi, Musa Usman, ya ce an rufe matatar ruwan ce saboda matsalar ingin wutar lantarki.
Ya ce akwai wasu manyan inji famfuna shida wadanda su ka kakare, sannan kuma akwai wani bututu da ya fashe, wanda ke kai ruwa wasu yankuna.
Ya ce ana kan kokarin gyara, amma ba zai iya cewa ga ranar da za kammala ba.
Discussion about this post