Matakai 5 da gwamnati za ta dauka domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa da kowa – Kwararru

0

Wasu kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa inganta shirin inshoran kiwon lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na cikin dabarun da za su taimaka wa gwamnati wajen cin ma burinta na samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa da kowa a kasar nan.

Wadannan kwararrun sun fadi haka ne a taron tsara hanyoyin inganta kiwon lafiya da NIPPS da DRPC-PAS suka shirya a Abuja.

Jami’in gidauniyar Bill da Melinda Gates, Paul Basinga ya bayyana cewa rashin ware isassun kudade domin inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, rashin ma’aikata, rashin ingantattun kayan aiki, gina asibitocin da ba za a iya kula da su ba, rashin saka mutane a cikin tsarin inshoran kiwon lafiya na daga cikin manyan matsalolin dake hana samun nasara a burin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa da kowa.

Domin kauce wa wannan matsalar ne Basinga ya zayyano wasu matakan da za su taimaka wa gwamnati wajen cin ma burinta.

1. Ware isassun kudade domin inganta fannin kiwon lafiya. Yin hakan zai hana yawan dogaro da tallafin da ake samu daga kungiyoyin bada tallafi.

2. Tsara ingantaccen hanyar da zai taimaka wajen samar da kudaden da ake bukata domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

3. Inganta tsarin inshoran kiwon lafiya domin talakawa su amfana.

4. Samar da inshoran kiwon lafiyar da zai kula da kiwon lafiyar mata da yara kanana.

5. Kara mai da hankali wajen kula da adadin yawan asibitocin dake kasar nan domin ganin cewa suna aiki yadda ya kamata.

Share.

game da Author