MARTANI GA OMOTOLA: Masu neman kudin halal ba su kukan kuncin rayuwa – Hadimin Buhari

0

Daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ya maida wa ’yar fim din Nollywood, Omotola martani dangane da kukan tsananin rayuwar kuncin da jama’a ke ciki a Najeriya.

PREMIUM TIMES ta ruwaito labari inda Omotola ya ta shiga shafin ta na twitter da kuma Instagram, ta bayyana cewa ‘yan Najeriya su na soyuwa a karkashin mulkin Buhari.

Ta kuma yi kukan cewa ana yawaita kashe mutane babu gaira babu dalili a ba yanki daya kadai ba, kusan ko a wane yankin kasar nan.

Omotola ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo su gaggauta kawo dauki musamman kan kashe-kashe da kuma bakin talaucin da ake fama da shi.

A na sa martanin da ya yi a shafin twitter na Omotola, Bashir Ahmad ya caccake ta a jiya Talata, inda ita ma ta biye masa, suka rika jifar juna da maganganu.

Bashir ya fara da cewa: “To Madam Omotola ai su wadanda ke neman halal a harkokin su ba ki jin su na kokawa, kuma ba za su taba cewa ana gasuwa a Najeriya ba.”

“A Kano kawai tsakanin 2015 zuwa 2018 an samu akalla kananan masana’antun casar shinkafa 200. Ta wannan hanyar kawai miliyoyin jama’a su na hada-hadar biliyoyin kudade.”

Haka Ahmad ya maida mata martani, inda daga nan kuma suka ci gaba, har jama’a su ka rika tofa albarkacin bakin su.

Cikin wadanda suka shiga batun har da Oby Ezekwesile, wadda ta goyi bayan Omotola, kuma ta ce ta ma daina damun kan ta a kan wannan gwamnatin.

Share.

game da Author