Fadar Shugaban Kasa ta maida martani ga Limamin Cocin Katolika, wanda y ace Shugaba Muhammadu Buhari bay a yin abin a zo a gani domin shawo kan kashe-kashen da ke faruwa a kasar nan.
A cikin takardar da Kakakin Buhari, Garba Shehu ya fiyar, fadar ta kuma zargi shugabannin da ke cikin jama’a cewa ba su son fallasa batagarin da ke cikin su ga jami’an tsaro.
Babban Limamin Katolika na Yola, Jihar Adamawa mai suna Stephen Mamza ne ya zargi Buhari, har aka mayar masa da wannan martani.
Mamza ya ce Buhari barcin sa kawai ya ke a matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.
Garba ya ce Shugaba Buhari ya yi matukar kokari wajen inganta tsaro a Arewa maso Gabas.
Daga nan sai ya ce ba Shugaba Buhari ne za a dora wa laifin kahe-kashen da ya haifar da asarar daruruwan jama’a a jihohi da yawa, ciki har da Adamawa, Taraba, Benue da Kaduna ba.
Ya ce shugabannin da ke cikin al’umma ne za a dora wa wannan laifin, na tashe-tashen hankula, ba Buhari ba.
“ Abin takaici dangane da abin da ke faruwa a Najeriya, a yanzu abu ne mafi sauki ka ji ana dora laifin tashe-tashen hankula a kan Buhari.
“ Shugabannin cikin jama’a ne ke da laifi, saboda tsoro suke ji su tona asirin manya da rikkun mabarnatan da ke cikin su, saboda su na gudun kada su ga bayan su.”
Shehu ya ce idan shugabannin da ke cikin al’umma ba za su rika fitowa su na fallasa rikakkun masu tayar da fitina da ke cikin su ba, to gwamnati ba za ta samu sukunin gudanar da gagarimin shirin dakile rikice-rikice ba a cikin sauki.
Ya yi kira da su taimaka wa gwamnati wajen fallasa mugayen da ke cikin jama’a, domin gwamnati ta gaggauta magance matsalolin kashe-kashen.