Marasa ilimin Boko sun kai miliyan 60 a Najeriya – Ma’aikatar Ilimi

0

Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi, Sonny Echono, ya bayyana cewa akwai marasa ilimin zamani kusan miliyan 60 a Najeriya.

Echono ya yi wannan bayani ne a jiya Alhamis a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Otobi, lokacin kaddamar da Cibiyar Yaki Da Jahilci ta Arewa ta Tsakiya.

Ya nuna rashin jin dadin yadda rashinn ilimin zamani ya yi wa matasa katutu da manya.

Sai ya ce gwamnati za ta yi matukar kokari domin ganin ta rage wannan wawakeken gibin sosai.

Ya ce irin yadda marasa ilmi ke karuwa a cikin matasa abin tsoro ne matuka.

Sai ya ce za a kafa Cibiyoyin Koyon Karatun Yaki da Jahilci a cikin Kwalejojin Gwamnatin Tarayya guda 104 a kasar nan.

Ya ce hakan zai rage matsalar a cikin malamai da kuma al’ummar yankuna.

Daga nan sai ya yi kira ga wadanda aka gina cibiyar domin su da su yi amfani da ita wajen inganta ilmin su da kuma tafiyar da al’amurran rayuwar su ta hanyar cin gajiyar ilmin da za su samu.

Ya ce ilmin da za su koya zai taimaka musu wajen cin nasarar duk wani kalubale da za su iya fuskanta na rayuwa.

Share.

game da Author