• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Gwamna Uba Sani ne ya yi  Ruwa ya yi Tsaki a takara ta ba mahaifina El-Rufai ba – Bello El-Rufai

    FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air

    Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto

    Atiku ya kafa gaggan lauyoyi 18, ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu

    SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Atiku ya zargi INEC ta ƙin ba shi kwafen bayanan zaɓe duk da ya biya haƙƙin Naira miliyan 6 kuɗin karɓar bayanan

    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

    Sojojin Najariya sun kara ragargaza wa Boko Haram motocin yaki bakwai

    Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

    HAJJI 2023: Yadda jirgin maniyyatan Jigawa ya koma Kano ba shiri, bayan ya samu matsala cikin sararin samaniyar Kamaru

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Maraba Da Watan Rahama, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
April 27, 2019
in Ra'ayi
0
Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Maraba Da Watan Rahama, Daga Imam Murtadha Gusau

Juma’ah, Sha’aban 20, 1440 AH (April 26, 2019)

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Bayan haka,

Ya ku ’yan uwana masu albarka! Ku sani, watan Ramadan yana daya daga cikin watannin da Musulmi suke haba-haba da zuwan sa a cikin watannin Musulunci. Wata ne da yake cike da alherai masu tarin yawa, wata ne da rahamomin da Allah Yake saukarwa a kan Musulmi suke yawaita. Domin Musulmi su kara samun rabo daga wadannan alherai da rahamomi, akwai bukakar su kintsa kansu matuka domin yin maraba da wannan wata, ta yadda za su shiga cikin sa cikin sauki tare da gudanar da ayyukan alheri masu yawa a daukacin watan.

’Yan uwana maza da mata! Yana da kyau Musulmi ya kintsa wa zuwan watan Ramadan tare da shirin aikata dukkan ayyukan kirki da ake so a cikin sa, domin samun alherai da rahamomin da ke cikin sa. Hudubar mu ta yau, za mu duba muhimmancin watan Ramadan ne da hanyar da Musulmi za su tunkare shi tare da kintsa masa kafin ya iso.

Muhimmancin Ramadan:

Ya ku bayin Allah! Akwai ayoyin Alkur’ani da Hadisan Annabi (SAW) da dama da suka yi magana kan muhimmancin Ramadan a Musulunci. Aya mai zuwa ta bayyana muhimmancin Ramadan kamar haka:

“Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, tsammanin ku za ku yi takawa.” [Kur’an, 2:183]

Daga wannan aya ta Alkur’ani Mai girma, za mu fahimci cewa azumi ba sabon abu ne ko wani abu na musamman da aka kebe Musulmi kawai da shi ba, maimakon haka, al’ummomin Annabawan da suka gabata ma sun yi azumi. Kuma a wannan aya Allah Madaukaki Ya bayyana manufar yin azumin watan Ramadan, wato mutane su samu takawa. Don haka azumi yana da muhimmanci ga Musulmi domin yana tsarkake ruhin sa tare da kai shi ga wani kololuwar matsayi na takawa.

Abin lura game da Ramadan:

Ya ku ’yan uwana! Duk lokacin da watan Ramadan yazo, abu na farko da ake so mutum yayi shine yayi nazari kan manufar azumin watan Ramadan. Allah Madaukaki ba Ya bukatar azumin kansa, ba Ya bukatar kishin ruwa ko yunwar wani Musulmi, maimakon haka azumin yana amfanar shi Musulmin ne da sauran al’ummah.

Kuma duk da cewa a ayar da muka ambata a sama, Allah Madaukaki Ya ambaci manufar yin azumi, cewa don Musulmi ya samu takawa. Duk da haka akwai wasu dalilai da za’a iya nazari kansu da za su iya kawo wasu manufofi na daban.

Na daya: a cikin watan Ramadan, dukkan Musulmi kan gudanar da ibadodi yadda ya kamata. Don haka sanannen al’amari ne cewa wannan wata yana bayar da damar dada samun lada da samun gafara kan zunubban da aka gudanar.

Na biyu: yunwa da kishin ruwan da ake sha a watan Ramadan suna taimaka wa Musulmi ya tuna da sauran mutanen duniya da ba su iya samun wadataccen abinci ko ruwan sha. Idan Musulmi yana yin azumi zai rika tuna wadancan mutanen, ya rika jin irin abin da suke ji, da yadda suke samun kansu na karancin kayan masarufi.

Na uku: a duk lokacin da Musulmi ya samu kansa a cikin rashin karfin jiki, duk da cewa yana shafar yanayin jiki, amma hakikanin abin da hakan ke haifarwa shine, gyara halin mutum ya zamo mai saukin kai da tawali’u da hakuri. Don haka a lokacin azumi, ana sa ran Musulmi yayi kokarin kyautata halayen sa wajen hakuri da tawali’u.

Kuma ina ba ku shawara ku yi kokari ku san umarni da hani kan azumin watan Ramadan yadda ya kamata, domin kauce wa aikata munanan abubuwa da kuma kokarin aikata kyawawa.

Kintsa wa Ramadan:

Musulmi sukan yi haba-haba da isowar Ramadan ta yadda za su rika gudanar da ayyukan Ibadah tare da samun dimbin albarka da rahama da gafarar Allah Madaukaki. Isowar Ramadan na kawo cikakken sauyi ko manyan sauye-sauye kan yadda mutum ke gudanar da rayuwar sa. Don haka wadanda ba su kintsa wa zuwan sa ba, sukan sha wahalar gudanar da ayyukan da Ramadan yake bukata a yau da kullum idan ya zo. Saboda haka manufar kintsawar ita ce mutum ya samu damar canja rayuwar sa zuwa daidai da rayuwar Ramadan, domin kada yayi asarar lokacin sa mai tsada. Bari in kawo manyan misalan abubuwan da za su taimaka wajen kintsa kanka domin samun alheran da suke cikin wannan wata mai girma.

Kyakkyawar niyya:

Farkon abin da ake bukatar Musulmi yayi game da kintsa wa Ramadan shine, kyakkyawar niyyah. Sai kayi niyyar aikata karin ayyukan alheri a wannan wata, za ka iya jin dadin Ramadan tare da samun alheran da yake kawowa. Amma idan kawai burinka ka shiga wata ka fice ba tare da aikata wani aikin alheri na daban ba, ko ka tsara yadda kawai za ka samu sauki ga kanka, to da wuya ka ci gajiyar Ramadan, kuma yana iya zama mai wahala a gare ka. Don haka yi kyakkyawar niyyah game da kintsa wa watan.

Sabo da yawan tasbihi:

Tasbihi shine yabon Allah Madaukaki da baki ko da harce da Musulmi zai yi, ta hanyar wasu jimloli ko kalmomi na ambaton Allah Madaukaki. A cikin watan Ramadan kowane lokaci na da muhimmanci, don haka idan mutum yana son samun lada mai yawa a ranakun Ramadan baya ga salloli, abin da yafi dacewa Musulmi yayi shine yayi ta Tasbihi. Idan ka fara Tasbihi wata daya kafin zuwan watan albarka na Ramadan, lokacin da watan zai zo tuni ka saba da yin Tasbihin, kana zaune ne ko kana tafe ko kana yin wani aiki.

Yin salloli a kowane lokaci:

Ya ku ’yan uwana maza da mata! A watan Ramadan, mutanen da suke halartar Sallah a cikin jama’a suna karuwa kwarai da gaske. Akwai mutanen da a farko sukan sha wahala kafin su samu su je Masallaci domin yin Sallah a cikin jama’a a farkon ranakun Ramadan. Domin ka tabbatar ka rika yin Sallah a cikin jama’a a ranakun farko na Ramadan, ka fara zuwa salloli cikin jama’a tun kafin Ramadan ya iso. Ga wadanda ba su san yadda ake yin Sallah yadda ta kamata ba, suna iya tuntubar malamai ko wadansu da suke kusa da su kan yadda ake Sallah mataki-mataki, ko su yi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da ke wayoyin su wajen dada fahimtar haka.

Kokarin yin azumin nafila:

Farkon azumin Ramadan kan zama mai wahala ga wadansu Musulmi, domin sukan hadu da yunwa da kishin ruwa ne kwatsam saboda ba su saba ba, kuma ba su san yadda za su wuni da karancin abinci ba. Ba su san yadda za su sauya rayuwar su game da cin abinci ko kishin ruwa ba. Yin azumin nafila ga irin wadannan kafin Ramadan zai taimaka musu kan yadda za su san sauye-sauyen da ke zuwa lokacin azumin ta yadda idan Ramadan ya zo sun kintsa masa.

Yawaita karatun Alkur’ani:

Karantun Alkur’ani na kawo albarka, da alheri, da zaman lafiya, da rufin asiri, da karuwar arziki, da kuma lada mai tarin yawa daga Allah Madaukaki; don haka yana da kyau Musulmi ya samu isasshen lokaci na karanta Alkur’ani. Ya tabbatar ya rika karanta Alkur’ani a watan Ramadan, kuma ya tabbatar ya saba da karatun sa kafin Ramadan ta yadda zai saba da karatun sa ko Ramadan ya zo. Ga wadanda ba su iya karanta shi cikin harshen Larabci, wannan ne lokaci mafi dacewa da za su fara koyon sa, saboda koyon karatun Alkur’ani a watan Ramadan yana da lada fiye da sau saba’in a kan koyon sa a wani wata na daban. A takaice yana da muhimmanci ga Musulmi ya kara zage dantse wajen sanin manufar azumin Ramadan ta yadda zai dada gogewa da aiwatar da wadancan manufofi a rayuwar sa. Kuma sanannen al’amari ne cewa kintsa wa wannan wata mai girma yana taimaka wa mutum ya ci gajiyar watan ta hanyar da ta fi dacewa.

Umarni da hani kan azumin Ramadan a takaice:

Ya ku Musulmi! Watan Ramadan Mai albarka yana daf da shigowa. Musulmi suna haba-haba da wannan wata mai girma, wanda a cikin sa suke Sallah da ambaton Allah Ta’ala suke samun alherai masu girma da lada mai yawa. Musulmi na azumtar wannan wata daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana ba tare da ci ko sha ko saduwa da iyali, da sauran su ba.

Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Idan watan Ramadan ya kama, akan bude kofofin Aljannah a kukkule kofofin wuta kuma a daure shaidanu.” [Buhari]

Wannan Hadisi na nuna cewa Ramadan watan neman gafara ne da samun albarka marar misaltuwa. Kuma kasancewar an daure shaidanu akan samu karancin barna a cikin watan. Baya ga haka, an nemi Musulmi su kaurace wa abinci da abin sha da wasu ayyuka, kuma ana bukatar su aikata wasu abubuwa a cikin Ramadan. Ga misalai daga ciki:

Abubuwan da ake so a aikata:

Ya kai bawan Allah! Akwai dimbin abubuwan da Musulmi zai yi da za su sa ya amfani alheran da suke cikin watan Ramadan kamar:

Karatun Alkur’ani a kullum – Abu na farko da za ka iya yi, wanda za ka tabbatar ka samu alherai da lada mafiya girma a wannan wata mai girma, shine karatun Alkur’ani. A kan kowane baki na Alkur’ani akwai lada, don haka gwargwadon abin da ka karanta daga Alkur’ani gwargwadon ladan da za ka samu. Kuma yana da kyau yayin karatun ya zamo kana hadawa da sanin ma’anonin sa, domin manufar karatun Alkur’ani shine hakan ya taimaka maka ka zamo Musulmi nagari ba a watan Ramadan kawai ba, a’a, a daukacin dukkanin watannin shekarun da za su biyo bayan sa.

Sauran sune yin sallolin nafila, da yawaita yin sadaka na nafila domin suna kawo lada mai yawa. Sai yin Sallar Tarawihi, da bayar da zakkah, da sada zumunci, da sauran ayyukan da’a da Allah yake so kuma ya yarda da su.

Abubuwan da aka hana ko ba’a so ayi a cikin watan Ramadan, sun hada da kauce wa cin abincin haram da rike mutum a zuciya wato rashin yafiya ga wanda ya saba maka da rashin hakuri da aikata ayyuka na shaidanci.

Akwai kuma kura-kurai da ake son mai azumi ya kauce musu da suka hada da fushi da yawan barci a wuni da yin azumi ba tare da yin Sallah ba, da furta kalamai ba tare da aunawa ba (wato yawan surutu marar amfani).

Manzon Allah (SAW) yace:

“Azumi garkuwa ne (daga wuta), don haka duk wanda yake azumi ya kauce wa munanan kalamai da ayyukan jahilci. Idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada ya ce masa: “Ni ina azumi! Ni ina azumi!” [Buhari]

A takaice ana so Musulmi a cikin watan Ramadan ya mayar da hankali wajen neman alherai da lada mai yawa iyakar karfin sa. Kuma yayi taka-tsantsan kan duk abin da zai yi tare da kauce wa duk abin da zai bata azumin sa ko ya hada shi gaba da husuma da mutane.

Yadda magabatan mu suke fuskantar watan Ramadan

An tambayi Ibn Mas’ud (RA)

Yaya ku Sahabai (RA) kuke fuskantar watan Ramadan? Yaya kuke shiga watan Ramadan??

Sai ya amsa da cewa:

“Babu wani daga cikin mu da zaya fuskanci watan Ramadan ko zai shiga watan Ramadan, face babu daidai da kwayar zarrah na hakkin dan uwansa, ko jin haushin dan uwan sa a cikin zuciyar sa.” [Shehun Malami Ibn Rajab Al Hambali ne ya ambaci wannan a littafin sa mai suna, LATA’IFIL MA’ARIF]

Don haka ya ku ‘yan uwana, muyi kakari mu yafewa junan mu, mu nemi afuwa a tsakanin mu, domin dacewa da alheran wannan wata mai albarka babu bakin ciki da damuwar wani a cikin zukatan mu.

Ni dai wallahi, dukkan wanda yayi man wani abu ko na sani ko ban sani ba wallahi na yafe masa, na yafe masa, na yafe masa.

Don Allah nima ku yafe mani, don Allah ku yafe mani, don Allah ku yafe mani.

Allah Ya taimake mu mu rayu kan koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Kuma Ya nuna mana gaskiya Ya bamu ikon bin ta, kuma Ya nuna mana karya (da bata) Ya bamu ikon kaurace musu. Amin.

Allah Ya kara tsira da aminci ga ManzonSa Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa.

Ina kammala wannan huduba tawa ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana dukkan zunuban mu, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.

Dan uwan ku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Ubete da Masallacin Marigayi Alhaji Abdur-Rahman Okene, da ke Okene Jihar Kogi, Najeriya. za’a iya samun sa ta: +2348038289761 ko kuma gusaumurtada@gmail.com

Tags: HausaImamImam Murtadha GusauLabaraiMarabaNajeriyaPREMIUM TIMESRamadan
Previous Post

Zango ya angonce duk da sanarwar dage auren sai bayan sallah da yayi

Next Post

Ko baza a canja Ministoci ba, Abuja na bukatar wayayye

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Ko baza a canja Ministoci ba, Abuja na bukatar wayayye

Ko baza a canja Ministoci ba, Abuja na bukatar wayayye

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHARI’AR ZABEN SHUGABAN ƘASA: Kotu ta karɓi sakamakon zaɓen jihohi 17 daga hannun Peter Obi domin tantance sahihancin su
  • TSAKANIN ATIKU DA KEYAMO: Keyamo ya ɗaukaka ƙarar hukuncin tarar Naira Miliyan 10 da Kotun Tarayya ta danƙara masa
  • KOTUN ZAƁEN SHUGABAN ƘASA TA ƊAU ZAFI: Yadda Atiku ya kaɗa hantar Tinubu, APC da INEC a zaman shari’ar ranar Laraba
  • Gwamna Uba Sani ne ya yi Ruwa ya yi Tsaki a takara ta ba mahaifina El-Rufai ba – Bello El-Rufai
  • Sanatoci 67 sun rattaba hannu Yari suke so, da karin wasu na nan tafe – Inji Abdul Ningi

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.