MANSUR DAN-ALI: Ministan Tsaro Ko ‘Ministan Tsoro’? Daga Ashafa Murnai

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mansur Dan Ali mukamin Ministan Tsarin Najeriya, cikin Oktoba, 2015. Ya fara aiki cikin Nuwamba, 2015.

Dan Jihar Zamfara ne. Dan Karamar Hukamar Birnin Magaji ne. Kuma dan gidan sarautar Masarautar Dan’alin Birnin Magaji ne. Kuma haifaffen daya daga cikin kananan hukumonin da mabarnata, mahara, ‘yan bindiga, ‘yan fashi, ‘yan samame, ‘yan darkake, makasa kuma masu garkuwa da mutane suka kassara.

Kenan, duk wasu shanun da aka sace, ko dukiyar da aka sace, ko kauyukan da aka banka wa wuta, ko ‘yan mata da matan da aka sace, ko dimbin mutanen da aka karkashe ko daruruwan wadanda aka yi garkuwa da su a tsakanin Nuwamba 2015 zuwa yau, cikin Afrilu, 2019, duk a zamanin ikon sa da shugabancin sa aka tafka wannan mummunar ta’asar.

Watanni 42, ba kwanaki 42 ba kenan ana ci gaba da tozarta al’ummar Jihar Zamfara, ana kashe na kashewa, ana sace na sacewa, ana tatsar makudan kudaden talakawa mazauna kauyuka ta hanyar biyan diyyar wadanda aka yi garkuwa da su. Ana hana mazauna kauyuka noma, ana kona kauyukan su. Ana tilasta masu yin hijira, duk a kan idon dan su, dan kauyen su, dan mahaifar su, dan gidan sarautar su, Mansur Dan Ali.

Mai karatu a dauka cewa a kauyen ku ko karkarar ku ce Ministan Tsaron Najeriya ya fito. Shin idan aka ce a kan idon sa kuma yanki ko karkarar da ya fito ce talakawa mazauna karkara suka fi fama da rashin tsaro, wace irin tutiya, tinkaho da takama za ku yi da shi?

Da shi da babu a mukami, ko akwai bambanci? Da irin wannan mukamin ba har gara a bai wa dan yankin ku sarautar Sarkin Turakun Kasuwar Birnin Magaji ba!

Mansur Dan Ali mutum ne da bai cika kazar-kazar ba. Sannan kuma bai cika magana ba. A irin yanayin da Jihar sa, Zamfara ke ciki, batun ya wuce Mansur ya zauna Abuja, ya na tura dakaru da kafa sansanoni a Zamfara ba.

Saboda duk da irin jami’an tsaron da ake ta jibgewa, har yau ba ka da wanda zai iya fitowa ya ce an samu sassauci a cikin Kananan Hukumomin da ake fitintinu a Zamfara.

Baya ga abubuwan da ke faruwa, har yau akwai titina a cikin jihar wadanda motoci ba su iya bi kwata – kwata.

Ka na gida an shigo an sace ka ko an sace wani na ka. Ka fita an tare ka an sace. Ka je wata kasuwar kauye an tare ka a hanya an bindige. Ka na barci an diro an banka wa kauyen ku wuta, an kuma bude muku wuta. Ba ka da sana’a sai noma. Ka je gona an yi garkuwa da kai. A gidan ka babu geron da za a daka fura tsawon kwana uku. To an yi garkuwa da kai, an sayar da gonakin ka da dabbobin da matar ka ke kiwo domin fita kunya a ranar auren ‘yar ka. Duk an tarkata kudaden an damka wa wadanda su ka yi garkuwa da kai.

Kuma wai duk abin nan dan karkarar ku ne Ministan Tsaro. Shin ina amfanin badi-ba-rai?

Ni dai ban sani ba ko Mansur Dan Ali ya karade dukkan kananan hukumomin da ake tashe-tashen hankula a cikin su, a cikin wadannan watanni 42 da ya yi ya na Ministan Tsaro. Idan ya je, shin ya kan keta cikin yankunan da ake tsoron ketawa?

Ko Dan Ali kan yini ya kwana a Birnin Magaji ko Maradun ko Anka ko Tsafe domin ji da ganin halin da ake ciki?

Zan yi murna, kuma zan taya Mansur Dan Ali farin ciki idan aka shawo kan wannan matsala ta Zamfara a zamanin ya na Minista. Kuma na san su ma ‘yan Jihar Zamfara za su so a ce a lokacin da dan su, ogan su, kanin su, yayan su, baban su kuma jini da asalin su ke Ministan Tsaro ne aka kashe wutar fitinar da ke neman gagarar su.

Cikin wannan mako, Mansur Dan Ali ya yi wani furuci da aka rika yi masa kallon kamar na ‘Ministan Tsoro’, maimakon irin na Ministan Tsaro.

Jama’a da dama sun cika da mamakin jin yadda Mansur ya fito ya ce akwai sa hannu da goyon bayan wasu sarakunan gargajiyar Zamfara a kashe-kashen da ake fama a jihar.

Tabdijan! Maganar gaskiya, babu wani dan Najeriya da ba zai yi mamakin jin yadda ka ke bada wannan labari a bainar jama’a ba. Sai har ma ka na cewa nan gaba za a fallasa su, kowa ya su.

A tunanin jama’a da dama shi ne, don me idan har gwamnati ta san da wadannan sarakunan gargajiyar ba za ta kamo su ba? Ina fa’idar ba mu labarin su, tunda ba ka sa an kamo su an fallasa su duniyar ta yi musu tofin Allah-wadai ba?

A irin wannan yanayi ranka ya dade, ai kawai aiki da cikawa mu ke son ji da gani daga gare ka. Amma furucin zargin wane ko su wance da su O’o, ba girman ka ba ne. Wannan zantuka ne na ‘yan kitimirmirar siyasa, irin su Lai Mohammed.

Ranka ya dade ba girman ka ba ne da a yanzu sarakunan Zamfara suka fito, su ka kalubalance ka cewa ka fito ka fallasa sarakunan da ka ce su na goyon bayan farmakin da mahara ke yi a Zamfara.

Shin za ka fito ka fallasa su din, idan har da gaske akwai su? Ko mirsisi za ka yi, kai shiru? Ko daka wasoson su za ka sa a yi? Ko kuwa hakuri za ka ba su a shafukan jarida?

Share.

game da Author