Majalisar Tarayya ta tashi daga zama ba shiri, saboda shigar-kutsen da ‘yan Shi’a suka yi

0

An tashi daga zaman Majalisar Tarayya na yau Laraba babu shiri, bayan da Mataimakin Kakakin Majalisa Yusuf Lasun ya bada sanarwa cewa mabiya Shi’a masu zanga-zanga sun barka fangamemiyar kofar shiga majalisa sun afka cikin farfajiyar harabar ginin.

Wannan sanarwa ta sa ’yan majalisa gaba daya suka rufe zama, wanda ake kan yi kafin a yi sanarwar.

Sama da shekara daya kenan mabiya Shi’a ke gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoran su Sheikh El-Zakzaky, wanda ke tsare tun cikin Disamba, 2015.

Su na gudanar da zanga-zangar a kullum in banda ranakun Asabar da kuma Lahadi.

Ana tsare da Ibrahim El-Zakzaky tun a ranar 12 Ga Disamba, 2015, tare da matar sa, bayan da sojoji suka bude wa mabiyan sa wuta a Zaari’a, Jihar Kaduna, aka kashe daruruwan mabiyan sa tare da ‘ya’yan sa.

An kafa kwamitin binciken rikicin, amma dai har yau ba a gurfanar da kowa dangabe da mabiya shi’a da aka kashe.

Babbar Kotun Tarayya ta sha bada belin El-Zakzaky domin ya fita shi da matar sa Zeenat su nemi magani daga ciwon da sojoji suka ji musu kafin a kama su, amma Gwamnatin Tarayya ta ki bada belin su.

An tabbatar da kashe mabiyan sa 347, sai dai kuma mabiyan san a ikirarin an kashe kimanin 1000.

Share.

game da Author