Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci, wato NSCIA, ta yi raga-raga da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN).
Wannan ya biyo bayan kiran da CAN ta yi wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya, inda ta nemi a bai wa Kiristoci manyan mukami a shugabannin majalisa.
Jiya ne CAN ta yi kiran cewa ba ta za ta yarda a ki bai wa Kiristoci ko da mukamin Shugaban Majalisar Dattawa ko na Tarayya ko kuma Mataimakan su ba.
Ta yi kira da kada a dankwafar da Kiristoci wajen rabon mukamai.
Ta buga misali da cewa Shugaban Kasa Musulmi ne haka ma Babban Cif Jojin Najeriya shi ma Musulmi ne.
A kan haka ne Majalisar Kolin Musulunci ta fito ta ragargaji CAN.
Da ya ke bayani a cikin wata takarda da ya fitar, Mataimakin Darakta Salisu Shehu, ya ce ya yi mamakin yadda CAN ta rikide ta koma ta na jagaliyancin siyasa.
Ya ce kalaman da CAN ta fitar rashin dattako ne, rashin sanin ya kamata, kuma zai iya kara rura su wutar raba kan ‘yan Najeriya.
Shehu ya ce amma bai yi mamakin bayanin ba, domin Kakakin Yada Labarai na CAN ne da kan sa, Adebayo Oladeji ya rubuta, a mamadin Shugaban CAN din.
Ya kara da cewa ya kamata CAN ta gaggauta zuwa ta yi rajista a matsayin ta na jam’iyyar siyasa. Domin tuni ta kauce daga Kungiyar Kare Manufofin Addini ta koma jagaliyancin siyasa.
Shehu ya ce bai ga kamfanin gaggawar yin kiran da CAN ta yi ba, in banda kokarin nuna kiyayya ga addinin Musulunci.
Ya ce wato ita CAN idan dai za ta biya bukata da naman ungulu, to babu ruwan ta da zabo duk kyawo da zakin naman sa kenan.
NSCIA ta kuma zargi CAN da nuna shiga sha’anin Alkalan Kotunan Shari’ar Kararrakin Siyasa, inda ta ce wa Kiristocin cikin su da su tausaya wa Kuristocin da aka kai kara a gaban su.
Wannan kuma NSCIA ta tunatar wa CAN yadda aka rika yi wa Musulmai rashin Adalci a Majalisar Tarayya, tun a baya farkon siyasar 1999.
Har yau, ta ma zargi Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya da yi wa Musulmai rashin adalci, kasancewa Kiristoci sun fi yawa a cikin su.
Discussion about this post