Shugaban Majalisar Tarayya, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Majalisa za ta saki Kasafin Kudi na 2019 a ranar Talata, 30 Ga Afrilu.
Jiya Laraba ne Saraki ya yi wannan sanarwa a Malajisa. Tun ranar Laraba ne aka tsara kammalawa da kasafin domin amincewa da abin da Kwamitin Majalisa na Kasafin Kudi ya gabatar, amma hakan bai yiwu ba.
Saraki ya ce bukatar kowane sanata ya kasance ya mallaki dalla-dallan bayanan kwamitin kasafin ne ya kawo aka dage zaman amincewa da kasafin kudin daga jiya Laraba zuwa ranar 30 Ga Afrilu.
Daga nan sai ya shaida wa sakatariyar ofishin Majalisar Tarayya cewa ofishin ya tabbatar da cewa ya wadatar da kowane sanata da kwafen bayanan kasafin kudin.
“Wasu mambobi ba su samu kwafen kasafin kudi ba, dalili kenan mu ka dage zaman kuma na umarci ‘Clerk’ na Majalisa cewa a tabbatar da kowane sanata ya mallaki kwafin kasafin kudin daga nan zuwa ranar Litinin. Idan aka yi haka, mu kuma ranar Talata sai mu saki kasafin kudin baki daya.
“Ba mu son shiga matsala, kada mu saki kasafin kudi, alhali wasu sanatoci ba su mallaki kwafe ba, daga baya kuma a zo ana maganganu. Amma idan kowa ya samu daga nan zuwa Litinin, to nan da zuwa Talata sai mu saki kasafin kawai.” Inji Saraki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sanarwar za a kashe Naira Tiriliyan 8.83 a kasafin kudi na 2019, wanda ya yi wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya bayani a ranar 19 Ga Disamba, 2018.
Discussion about this post