A yammacin Talata ne kakakin rundunar ‘yan sanda Najeriya Frank Mba ya sanar da ceto shugaban Hukumar UBEC ta kasa Abubakar Mahmood tare da ‘yar sa Yasmin da masu garkuwa suka sace.
Idan ba a manta a jiya Litinin ne mahara dauke da makamai suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja, inda suka bude wa motar shugaban hukumar UBEC na kasa wuta.
A wannan hari da suka kai, sun kashe direban sa sannan sun yi garkuwa da shi kan sa shugaban hukumar Mohammed Mahmood tare da ‘yar sa.
An aikata wannan abin tashin hankali ne a garin Katari, da misalin karfe 3:30 na yamma, kamar yadda wani hadimin Mahmood din ya sanar.
Kamar yadda Mba ya bayyana, an kuma kama wani mutum daya da ke da hannu a aikata wannan ta’asa.
Discussion about this post