Mahara dauke da muggan makamai sun far wa fitaccen gidan shakatawa dake garin Kajuru da ake kira ‘Kajuru Castle’ inda suka kashe wata ‘yar kasar waje da wasu mutane uku.
Maharan sun far wa wannan gida ne da misalin karfe 11:30 na safe ranar Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa maharan sun farwa wannan gida ne a daidai wasu masu yawon bude ido suna shakatawa a wannan gida ne.
A bayanan da ya bayar, ya kara da cewa bayan wannan ‘yar kasar waje da aka kashe da wasu mutane uku, sannan an yi garkuwa da wasu dake wannan gida a lokacin da aka kai harin.
Sabo ya ce wadannan mutane da ke yawon bude ido sun ziyarci wannan gari na Kajuru ne daga jihar Legas. Sai dai kuma har yanzu ba a iya sanin ko ‘yar wace kasa ce ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jigar Kaduna Ahmad Abdulrahman yayi kira ga mutane da su rika sanar da ‘yan sanda bayanan sirri game da ayyukan mahara idan an samu labarin su.