A wani hari da wasu mahara suka kai garin Kakangi dake karamar hukumar Birnin-Gwari, mutane da dama ne suka bace a gudun neman tsira da suka yi bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wannan gari da rana tsaka.
Shugaban Kungiyar duba gari na yankin Birnin-Gwari, Ibrahim Nagwari ya bayyana cewa a wannan hari, an kashe ‘yan sanda biyu sannan an cinna wa wani ofishin ‘yan sanda wuta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya bayyana cewa tabbas an kai wa garin Kakangi hari sannan maharan sun kashe sufeton ‘yan sanda Aliyu Mohammed da Sajen, Rabiu Abubakar.
Sabo ya bayyana cewa baya ga haka rundunar sa sun fatattaki maharan sannan sun kashe mutane uku cikin su kuma wasu da dama daga cikin su sun arce da raunuka a jikkunan su.
” Wani dan sanda mai suna Ibrahim Nasir da wasu mutanen gari shida suna asibiti kwance bayan tsira da suka yi da raunukan a jikkunan sa.
A karshe ya yi kira ga mutanen yankin da su zauna lafiya sannan su taimaka wajen tona asirin mafakan wadannan miyagun mutane.
Idan ba a manta ba Birnin-Gwari yayi kaurin suna a dalilin hare-haren ‘yan ta’adda da ayyukan masu garkuwa da mutane. Kusan kullum sai anyi garkuwa da matafiya a wannan hanya da kuma cikin garuruwan dake wannan karmar hukuma.
Ayyukan ‘yan ta’adda bai tsaya a nan ba kawai domin ya bazu ne har manyan titunan yankin Arewa Maso Yamma da ya kai ga titin Abuja zuwa Kaduna har ya kai ga ya na neman ya gagari matafiya.