Lallai Samun Nasara Yana Tare Da Hakuri, Daga Imam Murtadha Gusau
Litinin, Afrilu 08, 2019
Bismillahir Rahmanir Rahim
Dukkan yabo, godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Taimakon sa da gafarar sa muke nema. Kuma muna neman tsarin sa daga sharrin kawukan mu da munanan ayyukan mu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, lallai Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne.
Yaku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoron sa, kada ku mutu face kuna Musulmi.
Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijin ku wanda ya halicce ku daga rai guda daya, kuma ya halicci matar sa daga gare shi, kuma ya yada maza da mata daga gare su (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junan ku magiya da shi, kuma ku kiyaye zumunci. Lallai Allah mai kula ne da ku.
Yaku wandanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allah kuma ku fadi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukan ku, kuma ya gafarta maku zunubban ku. Wanda yabi Allah da Manzon sa hakika ya rabauta rabauta mai girma.
Bayan haka, lallai mafi gaskiyar magana ita ce maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu (SAW). Kuma mafi sharrin al’amura (a cikin addini) sune kagaggun su, kuma duk wani kagaggen abu (a cikin addini) bidi’a ce, kuma dukkan wata bidi’a bata ce, kuma duk wani bata yana wuta.
Bayan haka! Ya ku bayin Allah! Ku sani, Allah ya sanya hakuri ya zama tamkar wani ingarman dokin da ba ya tuntube, kuma tamkar takobin da ba ya dakushe wa, kuma tamkar wata rundunar da ba’a taba karya wa, kuma tamkar wata ganuwar da ba ta rusuwa. Don haka hakuri da nasara ‘yan uwan juna ne, kuma Danjuma ne da Danjumai, kuma duk mutumin da bai riki hakuri a matsayin makamin sa a addinin sa da duniyar sa ba, to yasan da sanin cewa, makiyan sa sai sun fatattake shi. Makiyi ne na zuciya ko na shaidan ne. Kuma babu wani karfi ga bawan da ba ya da hakuri. Kamar yadda babu shi babu cin nasara matukar dai ba shi da hakuri a yakin sa da yin gaba da abokin gaban sa. Allah Ta’ala yana cewa:
“Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure, kuma ku zama a cikin shiri, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta.”
Ya ku bayin Allah, hakika shi hakuri igiyar talala ce ta mumini, duk inda ya je zai komo gare shi.
Kuma shi dai hakuri ga mumini tamkar wata madogara ce da babu yadda ya iya sai ya dogara da ita. Babu imani cikakke ga wanda ba shi da hakuri. Duk sanda imani yayi karanci kuwa to sai ka ga ko da bautar Allah ma ta zama rabi-da-rabi. Ranar da gari yayi dadi sai ayi, ranar da kuma abubuwa suka cabe sai ayi biris da ita. Allah Ta’ala yace:
“Daga cikin mutane akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gaba, idan alheri ya same shi sai ya gamsu da shi, idan kuma wata musiba ta same shi sai ya juya baya, to wannan ya tabe duniya da lahira, wannan ita ce hasara mabayyaniya.”
Irin wannan bai samu komai a kasuwancin sa ba sai hasara mai girma da yayi. Wadanda suka dace da kyakkyawar rayuwa sun same ta ne a dalilin hakurin su. Don haka sun sami manya-manyan matsayi a dalilin godiyar su ga Allah. Sun ta shi sama da fikafikin hakuri da na godiya ga Allah zuwa ga Aljannar sa ta ni’ima. Saboda fadar Allah da yake cewa:
“Wannan falala ce daga Allah, yana bayar da ita ga wanda ya so, Allah kuwa Ma’abocin falala ne mai girma.”
Ya ku bayin Allah! Ku sani, shi hakuri halayyar cikakkun bayin Allah muminai ce, babu mai jure masa sai wanda Allah ya karfafe shi. Annabawa da Manzanni sune abin koyin mu, a dukkan nau’o’in hakuri, Imam Ahmad Dan Hanbal Allah ya rahamshe shi yace:
“Allah Mai tsarki ya ambaci hakuri sau casa’in a cikin Alkur’ani saboda muhimmancin sa.”
Sannan kuma Allah Mai girma da buwaya ya yabi masu hakuri a cikin littafin sa. Kuma Ya ba da labarin cewa ladar da zai ba masu hakuri, ta fi gaban lissafi, a inda yake cewa:
“Hakika masu hakuri ne kawai ake cika wa ladar su ba da lissafi ba.”
Bayan haka, kuma Allah ya fada cewa, yana tare da masu hakuri da shiriyar sa, da babban taimakon sa, da kuma bayyanannen budin sa. Yace:
“Ku yi hakuri, hakika Allah Yana tare da masu hakuri.”
Kasancewar masu hakuri suna tare da Allah, yasa suka rabauta da ni’imomin Allah na fili da na boye.
Haka kuma, bayan duk wadannan bayanai, Allah mai girma da daukaka, ya hada shugabanci a addini da hakuri da sakankancewa, a inda yace:
“Kuma muka sanya shugabanni daga cikin su (wato banu Isra’ila) suna shiryarwa da umarnin mu lokacin da suka yi hakuri, kuma sun kasance suna sakankancewa da ayoyin mu.”
Kari a kan haka, Allah ya rantse a kan cewa hakuri alheri ne ga masu yin sa, a inda yace:
“Kuma lallai idan kuka yi hakuri, to babu shakka shine mafi alheri ga masu hakuri.”
Kuma komai karfin abokin gaba, wallahi babu yadda ya iya da bawa mai hakuri da tsoron Allah. Allah madaukaki yace:
“Idan kuka yi hakuri kuka ji tsoron Allah, to makircin su ba zai cuce ku da komai ba. Hakika, Allah mai kewaye ne da sanin sa ga abin da suke aikatawa.”
Sannan kuma Allah Ya rataya rabautar bawa ga hakuri da jin tsoron sa. Sai Yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani kuyi hakuri, kuma ku jure, kuma ku zama a cikin shiri, kuma kuji tsoron Allah ko kwa rabauta.”
Bayan haka, kuma Allah Ta’ala ya bayyana kaunar sa ga bayin sa masu hakuri. Yace,
“Allah yana son masu hakuri.”
Sannan yayi wa masu hakuri albishir da abubuwa uku masu daraja fiye da abubuwan da bayi suke hassada a kansu a duniya. A inda yace:
“Kuma kayi albishir ga masu hakuri, wadanda idan wata masifa ta same su sai suce, mu na Allah ne, kuma mu a wurin sa za mu koma. Wadancan (bayi) gafarar Allah ta tabbata a gare su da rahama, kuma wadancan sune shiryayyu.”
Sannan kuma babu mai tsira daga wuta, kuma ya rabauta da Aljanna face masu hakuri. Allah mai girma da buwaya yace:
“Hakika ni ina saka masu a yau saboda hakurin su, hakika kuma sune masu rabauta.”
Kuma Allah ya kebance masu hakuri da godiya da amfanuwa da ayoyin sa inda, a in da don tantance su da wannan rabo mai girma, kuma gwaggwaba, har sau hudu a gurare daban-daban. Allah Ta’ala Yace:
“Hakika game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan hakuri mai yawan godiya.”
Duba surorin Ibrahim da Saba’i da Lukman da kuma Shura, za ka ga hakan.
Ya ku bayin Allah! Ku sani, ba wani abu ba ne hakuri face ka hana kan ka yin raki, da hana harshe kokawa, da kuma hana gabbai make-make da kekketa sutura da makamantan hakan.
Wani daga cikin nagartattun bayi ya ga wani mutum yana kai kukan matsalarsa ga dan uwan sa, sai yace da shi:
“To ai kai ka kai karar wanda zai tausaya maka (Allah) wurin wanda ba zai tausaya maka ba (Dan Adam).”
Wannan shi yasa aka ce, Mai kai kukan sa ga dan Adam yana kai kukan mai jin kai ne (wato Allah) wajen wanda ba zai ji kansa ba.
Ya ku bayin Allah! Ku sani, kai kuka iri biyu ne.
Na farko shine, kai kuka ga Allah. Wanda wannan ba ya korewa bawa hakuri. Kamar yadda Annabi Yakub yayi a lokacin da ya samu kan sa cikin damuwar batan Dan sa Annabi Yusuf. A inda yace:
“Ni fa kawai ina bayyana takaici na ne da bakin ciki na zuwa ga Allah. Kuma na san wani abu daga Allah wanda ku baku sani ba.”
Duk da haka kuma yace:
“Na yi hakuri kyakkyawa.”
Na biyu shi ne, wanda yake cikin wani bala’i ya rika nuna damuwar sa da maganar sa ko da yanayin sa. Irin wannan salo ya sabawa hakuri, yana ma rusa shi.
Manzon Allah (SAW) yace:
“Babu wata kyauta mafi yalwa da alheri da aka bai wa wani bawa irin hakuri.”
Shi hakuri tamkar linzami ne ga zuciyar dan Adam, da zarar aka rasa shi sai zuciya ta bazama.
Ya Ku bayin Allah! Ku sani, hakuri kashi uku ne, duba da abubuwan da suka rataya da shi.
Hakuri na farko shi ne, hakuri a kan bin Allah, da aiwatar da umarnin sa.
Hakuri na biyu kuwa, shine hakurin barin abubuwan da aka hana na sabon Allah.
Hakuri na uku kuma shine, hakuri a kan abubuwan da Allah ya kaddara kuma ya hukunta wa bayin sa, ta yadda bawa ba zai yi fushi da haka ba.
Sheikh Abdulqadir Jilani, Allah Yayi masa rahama ya fada a cikin littafin sa Fathul Gaib cewa:
“Babu makawa ga bawa har sai ya zama mai aikata umarnin Allah, ya kuma nisanci hanin sa, sannan ya yi hakuri da hukuncin Allah.”
Da wadannan kashi uku na hauri ne Lukman mai hikimah yayi wa dansa wasicci yace:
“Ya kai Da na, ka tsayar da Sallah, kuma kayi umarni da kyakkyawan aiki, kuma kayi hani da mummunan aiki, kuma ka yi hakuri bisa duk abin da ya same ka, lallai wannan yana daga cikin manyan abubuwa.”
Wayayyen mumini baya fatan bala’i ya same shi, sai dai yana hakuri da shi idan ya afku.
An karbo daga Abdullahi dan Abu Auf, Allah ya yarda da shi, yace: Hakika Manzon Allah (SAW) yace:
“Ya ku mutane kada ku yi fatan haduwa da abokan gaba, ku roki Allah zaman lafiya, sai dai idan kuka yi kicibis da abokan gaban to kuyi hakuri, kuma ku sani hakika Aljanna ta na karkashin inuwar takubba ne (wato bayan wuya sai dadi).”
Khalifan Manzon Allah, Abubakar Siddiq, Allah ya yarda da shi yace:
“Na fi son a kare ni da lafiya in gode fiye da a jarrabe ni da bala’i in yi hakuri.”
Don haka fatan afkuwar bala’i ba ya daga cikin koyarwar Musulunci. Amma fa idan bala’in ya afku, hakuri da shi ya zama dole. A koda yaushe al’amarin mumini alheri ne, ko dadi ko wuya, kamar yadda ya tabbata a cikin hadisin Sahih Muslim, daga Suhaibu dan Sinan ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce:
” Yi mamakin al’amarin mumini, hakika duk al’amuran sa alheri ne a gare shi, kuma babu wani wanda ya dace da haka sai dai muminin. Idan wani abin dadi ya same shi sai ya godewa Allah, hakan sai ya zamar masa alheri. Idan kuma wani abin ki ya same shi sai yayi hakuri, sai hakurin ya zama alheri a gare shi.”
Ya ku ‘yan uwa na masu girma! Ku sani, rayuwa dukkanin ta jarrabawa ce da gwaji. Allah Ta’ala yace:
“Muna jarraba ku da fitina, ta sharri da ta alheri, kuma gare mu za’a dawo da ku.”
Kuma ko da Allah yake jarraba bayin sa yana jarraba su ne domin ya gane masu hakuri daga cikin su, da jaruman su, da kuma masu gaskiyar su, daga wadanda ba haka ba. Allah Ta’ala yace:
“Kuna tsammanin za ku shiga Aljanna ne tun gabanin Allah bai san wadanda suka yi jihadi a cikin ku ba, kuma tun gabanin bai san masu hakuri ba.”
Kuma Allah yace:
“Kuma hakika wallahi za Mu jarrabe ku har sai Mun san masu jihadi daga cikin ku, kuma Mu san masu hakuri, kuma za mu jarraba ayyukan ku da zantukan ku.”
Da dai sauran ayoyi masu kama da wadannan.
Har wa yau, yana daga ckin hikimar da yasa Allah yake jarrabar bayi, don saukaka masu hanyar samun shahada, kamar yadda aya mai zuwa take sanar da hakan:
“Idan wani ciwo ko miki ya same ku, to hakika ciwo ko miki irin sa ya sami mutanen (a yakin Badar), wadancan kwanaki muna jujjuya su ne a tsakanin mutane, don Allah ya san wadanda suka ba da gaskiya (daga cikin ku) ya kuma sami shahidai daga gare ku. Allah kuwa ba ya son azzalumai. Kuma don Allah ya tsarkake wadanda suka ba da gaskiya, ya kuma hallakar da kafirai.”
Kuma Allah madaukakin sarki yace:
“Hakika dukiyoyin ku da ‘ya’yan ku fitina ne, kuma a wurin Allah lada mai girma yake.”
Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Annabi (SAW) ya kasance yana renon sahabban sa a kan yin hakuri da dukkan nau’o’in sa. Kuma hakan yana bayyana a fili karara idan muka dubi irin zaman Annabi da sahabban sa a garin Makkah.
An karbo hadisi daga Khabbab Dan Aratt. Yace; Mun kaiwa Manzon Allah (SAW) kuka, yana mai ta da kansa da wani mayafin sa a inuwar dakin Ka’abah. Sai muka ce masa, shin ba za ka nema mana taimakon Allah (a kan abokan gaban mu ba), shin ba za ka yi muna addu’a ba? Sai Annabi (SAW) yace:
“Tabbas cikin wadanda suka gabace ku a kan kamo mutum a haka rami a kasa a sa shi a ciki, sannan a zo da zarto a sa shi a kansa, a raba shi gida biyu, ko a rika tsefe naman jikin sa da matashin kai na karfe, amma duk da haka ba zai bar addinin sa ba. Na rantse da Allah al’amarin wannan addini zai cika har matafiyi ya tafi zuwa Hadaramaut (cikin kasar Yaman), daga Sana’a ba ya tsoron komai sai Allah. Sannan da fargabar kura ta far wa dabbobin sa. Sai dai ku kuna da gaggawa ne.”
Abin nufi a nan, yana umurtar su da suyi hakuri a kan addinin su, kamar yadda wadanda suka gabata suka yi hakuri. Kuma da sannu azabar da kafirai suka yi musu za ta gushe.
Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai ta kowane hali mutum ba ya wadatuwa daga yin hakuri, domin kuwa yana jujjuyawa ne tsakanin abin da ya wajaba yayi, da wanda ya wajaba ya bari da kuma abin da aka kaddara masa mai gudanuwa a kansa kwatsam. Ga kuma ni’ima da ta zama dole ya gode wa Allah a kanta. Idan kuma a koda yaushe bawa bai fita daga wadannan halaye ba hakuri ya zamar masa dole har zuwa ranar mutuwa.
Hadisai da maganganun magabata a kan falalar hakuri suna da yawa. Ga kadan daga ciki:
An karbo daga Ummu Salamah tace; na ji manzon Allah tsira da amincin Allah yana cewa:
“Babu wani Musulmi da wata masifa za ta same shi sai ya fadi abinda Allah ya umarce shi da shi, wato yace: “Daga Allah muke, kuma ga Allah za mu koma, ya Allah ka ba ni ladan jarrabawa ta kuma ka maye mani da abin da yafi ta. Face sai Allah ya maye masa da abin da yafi ta.”
Ummu Salamah ta ce, yayin da Abu Salamah (mijin ta) ya rasu sai na ce wane Musulmi ne yafi Abu Salamah, gida na farko da suka yi kaura zuwa ga Manzon Allah, sannan duk da haka sai na fada, sai Allah ya musanya mini da Manzon Allah (SAW).
An karbo daga Abu Hurairah, yace; hakika Manzon Allah (SAW) yace:
“Wanda Allah yake nufin sa da alheri, sai ya jarrabe shi.”
An karbo daga A’isha Allah ya yarda da ita tace: Manzon Allah (SAW) yace:
“Babu wata musiba da za ta sami mumini face sai Allah ya kankare masa laifukan sa ta dallilin ta, hatta daidai da kaya idan ya taka.”
Ya kai Dan uwa na Musulmi! Ka yi hakuri da makwabcin ka, da abokin zaman ka, ka yi masa alheri, kuma ka daurewa cutarwar sa. Sannan bayan haka kuma ka yi hakuri da wanda yake karkashin ka. Sannan dole sai an yi hakuri da iyali, don haka ka yi hakuri da matar ka a kan kura-kuren ta.
Ya ke ‘yar uwa ta mai daraja! Ke ma sai kin yi hakuri da mijin ki. Duk shugaba ma sai yayi hakuri da wadanda yake shugabanta. A dunkule dai hakuri ya zama dole ga dukkan mutane. Wanda yayi hakuri zai hadu da alheri mai dimbin yawa, wanda kuma ya rasa hakuri to hakika ya rasa alheri mai tarin yawa.
Ina rokon Allah dacewa gare ni da ku gaba daya, tare da neman taimakon sa a kan dukkanin alheri, domin shi mai cikakken iko ne a kan kowane abu.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Birnin Makkah, kasa mai tsarki. Za’a iya samun sa ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.
Discussion about this post