Daren jiya Laraba ne aka kammala wasan kafsawar farko a wasan kusa na karshen karshe, wato Kwata-Final.
Kungiyoyi takwas da suka rage a gasar su kafsa, kuma wasa ya nuna lallai Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool, a bana ma ba da wasa ta ke yi ba.
Da Liverpool Real Madrid ta buga wasan karshe cikin watan Mayu, 2018, inda aka yi nasara a kan Liverpool din da ci 3-1.
A jiya kuma Liverpool ya kwarara wa FC Porto kwallaye biyu, wadanda ke nuna cewa kulob din ya kama hanyar zuwa wasan kusa da na karshe, kafin zuwa wasan karshe da a za buga a sabon filin wasan Atletico Madrid, a Spain.
BARCELONA kuma ta je har Old Trafford, cikin gidan Manchester United, ta lallasa mata kwallo daya tilo.
Tabbas wannan ci daya zai kashe guyawun magoya bayan Manchester United, ganin cewa haduwar da kungiyoyin biyu suka yi say hudu a baya, babu wadda Man U ba ta sha kashi ba.
AJAX ta kwaci kan ta a hannun Juventus a gida, bayan an jefa mata kwallo daya.
Idan Ajax ta rike wuta a wasa na biyu a gidan Juventus, za a yi kare-jini-biri-jini. Wata kila ma Ajax din ta yi wa Juventus sakiyar da babu ruwa, irin wadda ta yi wa Real Madrid a wasan zagaye na biyu.
MANCHESTER CITY ta ci kasa a birnin Landan, inda Tottenham ta makala mata kwallo daya. Da wahala a ce ba ta rama kwallon ta har ta kara ba, idan aka je birnin Manchester a wasa na biyu.
Sai dai kuma ba a nan ta ke ba. Tottenham za ta iya buga wasan ko-a-ci-ko-a-mutu. Yadda ko dai idan an jefa mata kwallo ita ma ta rama, ko kuma a yi tashi canjaras, dayar da aka jefa wa Manchester City ta makale kenan.