Kungiyar Dattawan Kiristoci ta yi tir da ziyarar da CAN ta kai wa Buhari

0

Kungiyar Dattawan Kiristoci ta Najeriya (NCEF), ta yi tir da ziyarar da Kungiyar CAN ta kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaba a Abuja.

A cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin, dattawan sun ce wannan ziyarar ta nuna cewa CAN ta dade da kulla zumuncin da Ubangiji ya yi hani da shi tsakanin su da jam’iyyar APC.

Har yau dattawan dai kada a manta, Kungiyar Dattawan Kiristocin ta dade ta na sa-in-sa da CAN, wanda hakan ya janyo har CAN ta ce babu ruwanta da kungiyar dattawan kuma ta yanke mu’amala da su cikin Disamba da ya gabata.

To sai ga shi a cikin samarwar da dattawa suka bayar, sun ce Kungiyar CAN ta shiga cikin harkokin siyasa gadan-gadan. Ta kara da cewa CAN ta dauko hanyar da za ta ruguza Kiristanci nan gaba a Najeriya.

Sannan kuma sun sake nanata yin tir din su ga CAN da ta wakilta masu sa-ido har su 1,000 domin aikin sa-ido ga zabe.

Kungiyar Dattawan Kiristoci ta ce babu inda doka ta bai wa CAN izni ko ‘yancin nada masu sa-ido a harkar zabe.

Kungiyar kuma ta nuna rashin jin dadin kashe-kashen da ke faruwa a Arewacin kasar nan, musamman a Kajuru, cikin Jihar Kaduna.

Share.

game da Author