Kungiyar Daliban Jami’o’i ta Kasa (NANS), ta yi fatali tare da yin Allah-wadai da tsarin da Hukumar Kula da Man Fetur (NNPC) ta bi wajen daukar sabbin ma’aikata a kwanan nan.
NANS ta ce abin da NNPC ta nema daga ka’idojin da tilas wanda ke menan aikin zai cike, ba a tsara ka’idojin domin a dauki masu karamin karfi da kuma ‘ya’yan talakawa ba.
Jami’in Yada Labarai na NANS, Adeyemi Azeez ne ya fitar da sanarwar kin amincewa da matakan da NNPC ta dauka, a jiya Lahadi, kuma raba wa manema labarai.
Kungiyar ta ce da gangan aka gindaya sharuddan domin kawai a ture wadanda suka cika fam din neman dauka aiki a NNPC, musamman ‘ya’yan masu rangwamen gata.
Ya ce ai ba a banza ba yawan yajin aiki ya gurgunta harkokin ilmi a kasar nan.
Ya ce dalili kenan dalibin da zai je ya yi kwas na shekara hu, sai ya karke da zama har kusan shekaru 9 zuwa goma kafin ya kammala kwas din.
“Don haka NANS ba za ta yarda da wannan kullalliya da NNPC ta shirya domin hana wadanda suka cancanta da dama samun aikin ba.
Daga nan sai ya kara da cewa NANS ta bai wa NNPC sa’o’i 72, wato kwanaki uku da ta janye tsarin daukar ma’aikatan da ta fara, domin ba a shirya shi domin cin moriyar ‘ya’yan talakawa ba.
NANS ta ce idan ba a janye tsarin ba kuwa, za ta shiga yajin aiki, tare da fallasa duk wasu harkallar daukar ma’aikata da aka yi ak baya a cikin NNPC.
Kadan daga cikin tsauraran matakan da NNPC ta gindaya a matsayin sharudda, akwai:
Mai neman aikin ya kasance ya kammala jami’ar da Gwamnatin Tarayya ta amince da ita, amma banda wanda ya kammala jami’a kafin 2014.
Ya kasance mai neman aiki bai wuce shekaru 28 ba ya zuwa ranar 31 Ga Disamba, 2018.
Discussion about this post