Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta jaddada cewa ko dai Shugaban Majalisar Dattawa ko kuma Kakakin Majalisar Tarayya, to cikin su ya kasance daya Kirista ne.
CAN ta ce idan aka yi haka, to an gyara kuskuren rashin yin raba-daidai din mukaman siyasa a tsakanin addinai da ya faru a baya.
Shugaban CAN Samson Ayokunle shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na sa ya sa wa hannu a madadin sa.
Jami’in mai suna Adebayo Oladeji, ya bayyana haka ranar Litinin tare da cewa idan aka yi kamar yadda ya nemi a yi, to an yi adalci kenan, kuma an kauce wa yi wa wani addini rashin adalci.
Ya kara da cewa ita ma Dokar Najeriya ta 1999, cewa ta yi a rika yin rabon mukamai na siyasa ba tare da tauyewa ko dankwafar da mabiya wani addini ba.
Ayokunle ya ce idan aka yi haka, za a kauda zargin wani bangare na wani mabiya addini a Kan wani addinin daban a kasar nan.
Shugaban na CAN ya ce duk da cewa a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya akwai mukamai da dama, amma dai “inda mu ka fi maida hankali shi ne a batun Shugaban Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya. Sai kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya.”
“Saboda haka ake yi tun 1999, duk lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa ko ta Tarayya Kirista ne, zai kasance Mataimaki Musulmi ne. Haka idan Shugaba Musulmi ne, to Mataimaki zai kasance Kirista ne.”
“Amma an wayi gari a yau Shugaban Kasa Musulmi ne, sannan kuma Babban Mai Shari’a na Najeriya shi ma Musulmi ne. To irin wannan rashin yin raba-daidai ne mu ke kira da a kauce wa yi a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.