Ku Cewa Adam Zango Ya Daina Fariya Don Siffar Jahiliyar Farko Ce, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Akwai bambanci tsakanin mutum da maganarsa, shiyasa babu shakka idan malami yayi ashariya dole a kalli wannan aikin nasa a matsayin aikin maguzawa duk da cewa shi malami ne. Ko idan malami yayi zagi za a ce masa sadakallahul azim ne? Nasan duk biyayyar da ake yi masa ba za a fadi haka ba. Hakazalika idan bamaguje yayi kalmar shahada dole a Karba tunda zindiki ne yayi aikin mu’uminai.

Gaskiya Adam Zango yana bayyana ayyukan jahilan farko, nayi mamakin yadda ya mayar da fariya da bugun kirji abun yi. Wauta ce ace duk fadin arewacin Najeriya amma bai ji kunya ba yace wai yafi kowa suna a cikinta duk duniya. Shin yana da “Scientific research” ne akan haka? Saboda ganganci a wannan duniyar ta ilimi zaka fadi abu kuma a zira maka ido bayan malamai sunce babbar wauta a ilimi itace ka fadi magana babu hujja.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Wai shin ma ya san yadda ake samun hujjar yin generalization wato (jimlar abu wuri daya) a duniyar ilimi? Ko kuma kawai abun yanki-fadi ne? To idan haka ne nima sai nace duk duniya babu mai gangancinka. Tunda abun ya zama shegantaka.

Kada ya manta, babu shi ko a shafin bincike na (Goggle) idan aka neme shi “The most famous hausa actor in the world” sai dai Ali Nuhu. To wanne zamu yadda dashi daga ciki kenan? Maganarsa ko ta (Goggle)? Kada ka manta a arewa akwai su Dangote, Ahmad Musa da sauransu. Ban da kuma malamai da yan boko da siyasa. Ko National Bureau of Statistics (NBS) ce ta fadi cewa kafi kowa shahara a arewacin Najeriya? Ko kuma abun ya zama magori, to inada album din “Dan magori” na Nura M Inuwa kai aka yiwa. To ko a cikin “Top 5 2018 Kannywood actors babu kai, Ali Nuhu ne a sama. Kowa yaje yayi nema ya gani.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author