Kotun Sauraren Kararrrakin Zaben Gwamna, Majalisar Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kano ta bayyana cewa an shigar da kararraki 33 a gaban ta, wadanda duk tankiya ce a kan zabukan 2019 da aka gudanar.
Shugaban Kotun Mai Shari’a, Nayai Aganaba ne ya bayyana haka a lokacin da ake kaddamar da zaman kotun jiya Alhamis a Kano.
Ya ce dukkan kararrakin da aka karba su 33, duk na zabukan Majalisar Dokoki ne da kuma na Majalisar Tarayya.
Ya ce ya zuwa jiya Alhamis ba a kai ga shigar da kara kan zaben gwamna ba tukunna.
Anagaba ya roki jam’iyyun da ke cikin rigingimun shari’ar zabe da su bai wa kotu hadin kai, domin a tabbatar da cewa an gudanar da dukkan yanke hukunci a cikin kwanaki 180 da aka gindaya wa kotun cewa za ta kammala sauraren kararrakin.
Ya yi alkawarin cewa kotun za ta yi adalci, kuma ba za yi nuku-nuku ko nuna bangaranci wajen yanke hukunci ba.
Shi kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Ibrahim Muktar, ya tattabar wa alkalan cewa za a ba su wadatattun jami’an tsaro da kuma wurin da za su gudanar za zaman shari’a a inda ya kwanta musu a rai, ba tare da fuskantar wata barazana ba.
Shi ma Shugaban Kungiyar Lauyoyin Jihar Kano, Lawal Musa, ya ce lauyoyi za su bada hadin kai wajen ganin an samu nasarar da ta dace a samu a yayin zaman shari’un da za a yi.
Daga nan sai ya yi kira ga lauyoyi da su bai wa lokaci muhimmanci sosai ba tare da bata lokaci ko kawo jinkiri ba.
Hakan injin shi ya zama wajibi, domin kwanaki 180 kacal aka kebe domin a yi sauraron kararraki har zuwa yanke hukunce-hukunce.
Discussion about this post