Kotun majistare dake Aramoko jihar Ekiti ta yanke wa wasu mutane tara da aka kama suna yin bahaya a waje.
Kotun ta yanke musu hukuncin zaman kurkuku har na tsawon watani shida.
Laifukan da wadannan mutane suka aikata sun hada da rashin gina bandaki a gidajen su da rashin ajiye kwandon zubar da shara
Wadanda ake tuhuma sune, Olaleye Isaac, Ologun Ala, Agboola M, Atoro, Adetoyinbo, Adesoba Sunday, Jacob Taiwo, Titus Ibironke da Olu Obateru.