Ko baza a canja Ministoci ba, Abuja na bukatar wayayye

0

Tun bayan sauka daga kujeran ministan Abuja da gwamnan Kaduna na yanzu Nasir El-Rufai yayi babban birnin Tarayyar Najeriya ba ta sake samun ci gaban da za a iya bugun kirji da shi ba.

Baya ga kwarewa da yake dashi a kimiyyan tsara birane El-Rufai ya na da wayewa irin ta zamani da sanin yadda manyan biranen kasashen duniya ya kamata su kasance.

El-Rufai ya kakkafa tsare-tsare da saisaita Abuja da duk duniya ana alfahari da babban birnin Tarayyan Najeriya.

Sai dai kash, tun bayan saukar sa  daga  kujeran ministan Abuja babu wani minista da ya kwatanta irin abubuwan da ya yi a babban birnin.

Abin bakinciki da tashin hankali shine ganin yadda shirye-shiryen da ya tsastsara duk sun ragwargwabe. Sannu a hankali yanzu Abuja sai jagwabewa ta ke yi kamar ba babban birnin Najeriya ba.

Na farko dai duk inda ka bi yanzu zaka ga kazanta ta ne, musamman a unguwannin da da ba haka suke ba.

Kusan kowani layi kabi musamman a unguwannin Wuse, Wuye, Gwarimpa, kai hatta a tsakiyar gari zaka tsinci mai gasa doya a can, mai masara anan, masu talla kuwa da mabarata gasu nan burjik.

A lokacin El-Rufai zaka ga mutum bai isa ya ajiye motarsa a duk inda yaga dama ba amma yanzu kam wasu titinan ma zaka ga mutane sun rufe kaf  babu abinda ya dame su.

Abubuwa da dama an rasa su tun bayan tafiyarsa. Babban dalili kuwa shine na rashin samun wadanda suka biyo bayan sa masu ilimi da fahimtar tsara manyan birane da wayewa da sanin yadda biranen kasashen da suka ci gaba suke.

Aliyu Modibbo, ya biyo sahun El-Rufai sai dai kash, hakansa bai kai ga cimma ruwa ba domin bai dade akan kujerar ministan ba aka canja shi.

Modibbo yayi zaman kasar Amurka kuma yana da kwarewa a harkar sanin tsare-tsare da inganta birane a dalilin dadewar dayayi a kasashen waje.

Yanzu dai gwamnatin Muhammadu Buhari na bukatan ta yi wa Abuja goma ta arziki ta nada mata ministan da zai dawo da harkar sufuri na gwamnati a garin Abuja da kewaye kamar yadda take ada. A nada wanda zai gina ta da tsara ta kamar yadda manyan biranen wasu kasashen duniya suke.

Idan dai za a yi wa Abuja adalci, dole ne gwamnati ta zabo ministan da ya san abubuwan da ya kamata ya kafa a babban birnin.

Daga, Ummi Mohammed, Wuye Abuja

Share.

game da Author