Ko ba ka yi sakandare ba doka ta yarda ka shugabancin Najeriya – Keyamo

0

Kakakin Jam’iyyar APC, na Kamfen din Shugaban Kasa, Festus Kiyamo, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a Najeriya ba ya bukatar sai ya mallaki Kwalin Shaidar Kammala Sakandare.

Haka dai Keyamo ya rattaba a shafin sa na Twitter mai suna @fkiyamo, jiya Litinin.

A cewar sa, “matsawar dan takara ya dade ya na rike da wani babban mukami a kasar nan, to idan zai yi takarar shugaban kasa ba shi ma bukatar takardar shaidar kammala sakandare (WAEC).”

“Amma akwai sauran matakai da ka’idojin da doka ta tanadar idan za ka tsaya takarar shugaban kasa. Sai dai kuma matsawar ka taba rike wani mukami tsawon lokaci a kasar nan, to ba ka bukatar katin shaidar kammala sakandare, wato WAEC.”

A zabukan baya an sha wannan gwagwarmayar zargin Shugaba Muhammadu Buhari bai kammala sakandare ba. an kuma ce bai mallaki satifiket na WAEC ba.

Share.

game da Author