A jiya Alhamis ne Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da wasu ‘Yan Majalisa 51 suka kawo tsaiko ga karar da aka kai su, inda aka nemi su sauka daga kujerun su, tunda sun canja shekara daga APC zuwa PDP.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ke karkashin Mai Shari’a Okong Agban, ta tsaida jiya Alhamis ce ranar da za ta yanke hukunci a kan karar.
Wata Kungiyar Kare Dimokradiyya ce mai suna LEDAP ta shigar da kara tun a ranar 14 Ga Satumba, 2018.
LEDAP ta nemi kotu ta yanke hukunci, shin daidai ne ‘yan majalisar su ci gaba da zama a kan kujerun su, tunda APC ce ta zabe su ba PDP din da suka koma ba?
Cikin watan Yuli, 2018 ne ‘Yan Majalisar Tarayya 37 su ka fice daga APC, inda 32 suka koma PDP, 4 kuma ADC.
Washegari kuma Sanatocin APC 14, ciki har da Saraki suka koma PDP.
Dalili kenan LEDAP ta kai kara inda ta nemi kotu ta tsige su daga kan kujerun su, tunda sun fice daga jam’iyyar da su ke wa wakilci.
Sai dai kuma yayin da aka yi zaman yanke hukunci a jiya Alhamis, sai lauyan su Saraki mai suna Mahmood Magaji, ya ce bai kamata a yanke hukunci ba, domin Mai Shari’a bai ji ba’asin bangaren wadanda ake kara ba.
Ya ce bayanan kararrakin da ake yi wa wadanda ya ke karewa bai je musu da wuri ba, ya isa gare au a kurarren lokaci.
Mai Shari’a Okon Abang ya ce da lauyan su bai yi fashi ba, da sun samu bayanan da wuri. Da farko lauyan LEDAP ya cirje cewa bai kamata a kara musu wa’adin da suka nema ba.
Amma Mai Shari’a Abang ya ce za a zauna yau Juma’a domin a saurari tafka muhawarar neman karin lokacin.
Discussion about this post