Kashi 90 bisa 100 na shinkafar da ake ci a Najeriya, a nan ake noma ta – Ministan Gona

0

Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Audu Ogbe, ya nuna gamsuwar sa ganin a yanzu a cewar sa a Najeriya ake noma kashi 90 bisa 100 na shinkafar da ake ci a cikin kasar nan.

Ogbe ya bayyana haka ne a yau a wurin Taron Shekara-shekara na Bincike da Tsare-tsaren Dabarun Noma na 2019.

An shirya taron ne a Dakin Taro na Balarabe Tanimu da ke Cibiyar Binciken Dabarun Noma (IAR) da ke Zaria, Jihar Kaduna.

Taken taron shi ne: “Rawar Da Masu Ruwa da Tsaki Za Su Iya Takawa, Wajen Samar Da Albarkatun Gona Domin Fitarwa Kasashen Ketare”.

Daya daga cikin daraktaocin Ma’aikatar Harkokin Gona, Karima Babangida ce ta wakilci minista Ogbe.

Ta ce hukumar ta taimaka wa gwamman gwamnati wajen samar da abincin da za mu rika ci a gida Najeriya, maimakon dogaro da shigo da abinci daga waje.

“Najeriya a yanzu ta kai matakin da ba wai abincin ciyar da kanta kawai za ta iya nomawa ba, ta ma zama daya daga cikin manyan kasashen da ke Afrika, Kudanci da Arewacin AMURKA, Turai da kuma China masu noma abinci a duniya.

Daga nan sai ministan ya yi kira da a kara yawan samfuran abincin da ake nomawa tare da kara maida hankali wajen kiwon kifi, dabbobi, ‘ya’yan itatuwa da sauran su.

Share.

game da Author