Kashi 2 bisa 3 na masu fama da yunwa a duniya su na Najeriya da wasu kasashe bakwai – UN

0

Majalisar Dinkin Duniya (UN), ta bayyana cewa akalla akwai mutane miliyan 113 a fadin duniyar nan masu fama da matsananciyar wahalar rashin abinci.

Wata kididdiga ce da aka yi cikin 2018, sannan aka fitar da bayanan ta a cikin 2019 ta tabbatar da haka.

An fitar da wannan bincike a birnin Brussels, babban birnin kasar Belgium a yau Laraba, tare da yin kakkausan gargadin cewa matsalar abincin ta samu sanadi ne daga rikice-rikice da kuma annoba da bala’o’in da ake fuskanta a wasu yankuna.

Rahoton ya zurfafa bincike inda kuma ya gano cewa wannan matsalar yunwa da rashin abinci, ta fi yin katutu ne a cikin kasashe takwas.

Wadannan kasashen su ne; Afghanistan, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Ethiopia, Najeriya, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria da Yemen.

“Wadannan kasashe takwas sunn kunshi kashi biyu bisa uku na ilahirin wayan al’ummar da yunwa ta kassara suka cikin mawuyacin hali a duniya. Kusan mutane milyann 72 kenan.’ Haka rahoton ya bayyana.

Sannan kuma rahoton ya kara nuna fargabar cewa wadannan kasashe, wato Najeriya ta Arewa, Afghanistan, DRC, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria, Ethiopia da Yemen za su kasance cikin wannan hali a yanzu cikin 2019.

Rahoton ya ruwaito cewa Jihohi 16 na Arewacin Najeriya har da Yankin FCT, cewa yawan wadanda suka shiga cikin matasalar abinci ta ragu zuwa da kashi 40 bisa 100 tsakanin 2017 da 2018, zuwa mutane milyan 5.3.

Babban Daraktan Hukumar Abinci da Harkar Noma ta Duniya (FAO), Jose da Silva, ya shaida cewa duk da yawan masu fama da yunwa din ya ragu a cikin 2018, to har yanzu yawan adadlin wadanda ke cikin kunci abin tayar da hankula ne kwarai.

Ya de akwai bukatar hukumomi da kungiyoyin jin kai na duniya su sa hannu domin gaggauta rage wannan matsala.

Jose da Silva ya buga misali da halin kuncin rayuwar da ake ciki a yankunan da Boko Haram ya yi wa ta’adi da babbar illa.

Share.

game da Author